Dakatar da sakataren gwamnati: Osinbajo da Babachir sun sa labule

Dakatar da sakataren gwamnati: Osinbajo da Babachir sun sa labule

- Jim kada bayan an sanar da dakatar da sakataren gwamnati Babachir David daga aiki sai ya ruga ofishin mataimamin shugaban kasa

- Babachir bai bayyana yan jaridu abin da suka tattauna ba

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da sakataren gwamnati jim kada bayan an sanar da dakatar da shi daga aiki.

Kamfanin dillacin labaru, NAN, ta ruwaito ganawar sirrin data wakana tsakanin Osinbajo da Babachir na da alaka da aikin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa mataimakin nasa tare da ministan shari’a da kuma mai bashi shawara akan lamurran tsaro na su binciki Babachir din.

KU KARANTA: Dubi yadda Babachir ya tattara ya bar fadar shugaban kasa

Sai dai yaki ya bayyana ma yan jaridu komai bayan ya fito daga ofishin mataimakin shugaban kasar.

Dakatar da sakataren gwamnati: Osinbajo da Babachir sun sa labule

Babachir David

Haka zalika shima shugaban hukumar liken asiri, NIA Mista Ayo Oke an hange shi a harabar ofishin mataimakin shugaban kasar, mintuna kadan bayan tafiyar Babachir, sai dai daya hangi yan jaridu sai ya nemi ya canza hanyar fita, amma jami’an tsaro suka hana shi.

Rahotannin da suka ishe NAIJ.com sun tabbatar da cewar Oke bai samu ganin mataimakin shugaban kasar ba.

Dakatar da sakataren gwamnati: Osinbajo da Babachir sun sa labule

Ayo Oke yayin dayake kuka bayan an hana shi ganin mataimakin shugaban kasa

A ranar Laraba 19 ga watan Afrilu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bakin mashawarcin sa kan harkokin watsa labaru, Femi Adesina ya sanar da dakatar da sakataren gwamnati Babachir David Lawal tare da shugaban hukumar liken asiri ta kasa, Mista Ayodele Oke.

Shugaba Buhari ya bada umarnin a gudanar da cikakken bincike kan makudan kudaden da aka bankado a wani katafren gida dake jihar Legas, wanda hukumar liken asirin tayi ikirarin cewa nata ne.

Binciken da Buhari ya bada umarnin a gudanar ya hada da gano yadda NIA ta mallaki wadannan makudan kudade, ta yaya, way a basu da kuma umarnin waye ya basu kudin, sa’annan shugaba Buhari ya bukaci a gano an karya doka a hakan ko kuwa?

Ga bidiyon yadda Babachir ya fice daga fadar shugaban kasa a ranar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani dan Najeriya ya gargadi gwamnati zai fara sata:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel