Dubi yadda Babachir ya tattara ya bar fadar shugaban kasa

Dubi yadda Babachir ya tattara ya bar fadar shugaban kasa

– Shugaba Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin sa

– Shugaban kasan ya sa ayi bincike game da Babachir David Lawal

– Haka nan kuma an dakatar da shugaban Hukumar NIA

Dubi yadda Babachir ya tattara ya bar fadar shugaban kasa

Babachir ya bar fadar Villa jiya

A jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin sa Mr. Babachir David Lawal bisa zargin bada kwangiloli ba daidai ba kwanakin baya. NAIJ.com ta kawo ce kuma za a binciki Sakataren Gwamnatin.

Har ila yau Shugaba Buhari ya dakatar da shugaban Hukumar NIA mai leken asiri na kasa da Ambasada Ayodele Oke bayan Hukumar EFCC ta bankado wasu makudan miliyoyin daloli da yace na Hukumar ne. Oke dai ya fashe da kuka lokacin da aka hana sa ganawa da shugaban kasa.

KU KARANTA: Babachir ya rude bayan an ce an dakatar da shi

Dubi yadda Babachir ya tattara ya bar fadar shugaban kasa

Mr. Babachir David Lawal ya tattara kayan sa ya bar fadar shugaban kasa

Dakatarwar ta zo da ban mamaki ga Babachir David Lawal wanda ya tsaya yana tambayar ‘yan jarida cikin mamaki. Tuni dai shugaban kasar ya bada umarni wani ya rike kujerar har zuwa lokacin da za a gama bincike bayan mako biyu.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da kuma mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro da Ministan shari’a za su yi bincike game da lamarin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jama'a sun kai kuka wurin Gwamnati

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel