Rundunar yan sanda ta fara binciken jifar da akayi wa Sanata a Katsina

Rundunar yan sanda ta fara binciken jifar da akayi wa Sanata a Katsina

- Rundunar yan-sandan jihar Katsina ta fara gudanar da bincike akan mafusatan matasan da suka jefi motar gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari

- Matasan sun kuma cin zarafi da fasa motar sanatan Katsina ta Kudu Sanata Abu Ibrahim, da kuma dan majalissar wakila Aminu Tukur mai wakiltar Bakori da Danja

NAIJ.com ta tsinkayi Mai magana da yawun yansandan jihar Isah Gambo yana tabbatar wa majiyarmu cewa tuni suka fara bincike a kan harin da aka kai masu.

Ya bayyana cewa abin da kawai ya sani shi ne duk wani mai hannu a cikin harin za a cafko shi, in bincike ya tabbatar da hannunsa a ciki za a hukunta shi.

Sai dai Yanmajalissun Sanata Abu Ibrahim da Aminu Tukur duk sun musanta cewa an jefe su ko an fasa masu motoci, a sanarwar da suka fitar ta bayan taron.

Rundunar yan sanda ta fara binciken jifar da akayi wa Sanata a Katsina

Rundunar yan sanda ta fara binciken jifar da akayi wa Sanata a Katsina

A wani labarin kuma, Valentine Obienyen mai taimakawa tsohon gwamnan jihar Anambra Mista Peter Obi kan kafofin yaɗa labarai yace jami’an hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzkikin ƙasa ta’annati, EFFC sun kai sumame gidan tsohon gwamnan bayan da aka gano $43 a kusa da gidan da yake zaune a Legas.

KU KARANTA: Shugaban NIA ya fashe da kuka bayan da Shugaba Buhari ya dakatar da shi

A wata sanarwa Obienyem yace Obi da matarsa sun karbi hayar gidan da aka kai sumamen kuma suna zama a ciki a duk lokacin da sukaje birnin Legas.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli ra'ayoyin mutane game da shirin kwarmato

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi

Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi, ya shekara 5 kenan rabonsu da ko waya

Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi
NAIJ.com
Mailfire view pixel