Madalla! Cutar Sankarau ta fara lafawa a Arewa

Madalla! Cutar Sankarau ta fara lafawa a Arewa

- Gwamnatin Najeriya ta ce kimanin mutane 745 suka mutu sakamakon annobar Sankarau a sassan kasar

- Kuma cikin mako an samu mutane 250 da suka mutu yayin da a yanzu sama da mutane 8,000 ke kwance a asibiti a jihohi 19

Amma yanzu an fara samun lafawar cutar a yankunan da ta fi kamari kamar Zamfara da Sakoto.

NAIJ.com ta tattaro a wani labarin kuma cewa Kwamitin tallafawa al’ummar arewa maso gabas da ke karkashin Janar Theophilus Danjuma ya gana da kwararru don tara karin bayanai hanyoyin shawo dukkan kalubalen da al’ummar yankin ke fuskanta daidai lokacin da su ke farfadowa daga illar Boko Haram.

Taron wanda ya gudana a Hotel din Custodian dake garin Gombe a jihar Gombe da ke tsakiyar jihohi 6 na yankin, ya samu halartar farfesa Jibrin Ibrahim wanda ya nanata batun iyaye su rika cusa tarbiyya a zukatan yara don hana su kangarewa in sun girma.

Madalla! Cutar Sankarau ta fara lafawa a Arewa

Madalla! Cutar Sankarau ta fara lafawa a Arewa

NAIJ.com ta samu labarin cewa Farfesa Ibrahim ya kara da cewa ya zama wajibi al’ummar yankin su kara jajircewa da kula da duk bakin da kan shigo yankin su don tantance na gari da mugu.

KU KARANTA: Mako biyu kenan ba'a ga Buhari ya fito

Hakanan Farfesan ya ba da shawarar gina gidaje a waje daya maimakon yadda kauyuka su ke da gidaje da ke jefe da tazara da juna da hakan kan ba wa ‘yan ta’adda damar dauki daddaya ga jama’a.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel