Kwamitin tallafin shugaban kasa na Arewa maso gabas ya fara aiki gadan-gadan

Kwamitin tallafin shugaban kasa na Arewa maso gabas ya fara aiki gadan-gadan

- Kwamitin tallafawa al’ummar arewa maso gabas da ke karkashin Janar Theophilus Danjuma ya gana da kwararru

- Sun gana da su ne don tara karin bayanai hanyoyin shawo dukkan kalubalen da al’ummar yankin ke fuskanta daidai lokacin da su ke farfadowa daga illar Boko Haram

Taron wanda ya gudana a Hotel din Custodian dake garin Gombe a jihar Gombe da ke tsakiyar jihohi 6 na yankin, ya samu halartar farfesa Jibrin Ibrahim wanda ya nanata batun iyaye su rika cusa tarbiyya a zukatan yara don hana su kangarewa in sun girma.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Farfesa Ibrahim ya kara da cewa ya zama wajibi al’ummar yankin su kara jajircewa da kula da duk bakin da kan shigo yankin su don tantance na gari da mugu.

Hakanan Farfesan ya ba da shawarar gina gidaje a waje daya maimakon yadda kauyuka su ke da gidaje da ke jefe da tazara da juna da hakan kan ba wa ‘yan ta’adda damar dauki daddaya ga jama’a.

Kwamitin tallafin shugaban kasa na Arewa maso Gabas ya fara aiki gadan-gadan

Kwamitin tallafin shugaban kasa na Arewa maso Gabas ya fara aiki gadan-gadan

Mataimakin shugaban kwamitin Alhaji Tijjani Tumsa ya yi alwashin ci gaba da aiki tukuru don tallafawa al’ummar yankin musamman wadanda su ka rasa matsugunan su, su koma garuruwan su na asali.

KU KARANTA: Yaki da cin hancin Gwamnatin Buhari duk hira ce - Sule Lamido

Tumsa ya ce kwamitin zai bullo da hanyoyin yaki da talauci don yankin na kan gaba wajen fama da kuncin talauci a Najeriya.

Sauran wadanda su ka yi sharhi sun ba da misalin tasirin sanya idon al’umma da ya tallafa wajen dakile illar ‘yan Boko Haram a garin Biu da kuma jihar Jigawa duk da su na yankunan da ‘yan ta’addan su ka yi wa kaka-gida.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma ana gangamin ganin an kwato yan matan da aka sace

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel