Champions league: An yi waje da Kungiyar Barcelona

Champions league: An yi waje da Kungiyar Barcelona

– Barcelona tayi waje daga Gasar UEFA Champions league

– Juventus ta doke Barcelona tun a zagayen farko

– Wannan karo an tashi 0-0 ba tare da ci ba

Champions league: An yi waje da Kungiyar Barcelona

Champions league: Juventus ta kora Barcelona

An yi waje da Kungiyar Barcelona daga daga Gasar UEFA Champions league na zakarun Nahiyar Turai na kakar bana a jiya inda su ka fafata da Juventus. Yanzu Juventus ta karasa zagaye na gaba.

An dai tashi wasan ne babu ci sai dai a karo na farko Juventus sun doke Barcelona da ci 3-0. A wancan karo Dan wasa Dybala ne yayi tashe. Wannan karo dai Barcelona sun yi kokarin rama kwallayen amma Juventus su ka kare ragar su.

KU KARANTA: UCL: Madrid ta doke Bayern Munich

Champions league: An yi waje da Kungiyar Barcelona

Juventus sun yi Kungiyar Barcelona tauri

A zagayen baya Barcelona ta fitar da PSG bayan da farko ta sha mugun kashi wannan karo dai duk da ‘Yan wasan Barcelona abin ya faskara. Dama can NAIJ.com ta kawo maku cewa Real Madrid sun yi waje da Kungiyar Bayern Munich daga Gasar a wasan Ranar Talata.

Dortmund ta yi waje bayan da Kungiyar Monaco ta kara lallasa ta da ci 3-1. Yanzu dai ba wata Kungiyar Jamus da Ingila a Gasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Efa yayi nasara a Gasar Big Brother

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel