Jami'an gwamnati sun karkatar da biliyoyin kudi – Shehu Sani

Jami'an gwamnati sun karkatar da biliyoyin kudi – Shehu Sani

- Shugaban kwamitin majalisar dattijai da ya binciki zargin karkatar da tallafin 'yan gudun hijira ya ce matakin dakatar da sakataren gwamnatin tarayya ya nuna cewa Buhari ya dauki hanyar ba-sani-ba-sabo

- Sanata Shehu Sani ya ce jami'an gwamnati sun karkatar da biliyoyin kudin da aka ware don taimaka wa 'yan gudun hijira

- Ya ce shugaba Buhari ya nuna wa 'yan Najeriya cewa ko da dansa ko amininsa ne ya kauce wa hanya ta fuskar cin hanci da rashawa zai yi maganinsa

Shugaban kwamitin majalisar dattijai da ya binciki zargin karkatar da tallafin 'yan gudun hijira, ya ce matakin dakatar da sakataren gwamnatin tarayya ya nuna cewa Buhari ya dauki hanyar ba-sani-ba-sabo.

Sanata Shehu Sani ya ce jami'an gwamnati sun karkatar da biliyoyin kudin da aka ware don taimaka wa 'yan gudun hijira.

"Mun gano cewa biliyoyin kudade da ya kamata a yi amfani da su wajen taimaka wa marayu, 'yan gudun hijira da yawa an kau da su. Jami'an gwamnati sun sa a cikin nasu jakunkuna."

Jami'an gwamnati sun karkatar da biliyoyin kudi – Shehu Sani

Shehu Sani yace Jami'an gwamnati sun karkatar da biliyoyin kudi zuwa jakunkunan su

A cewarsa kafin wannan lokaci zargin da ake yi shi ne idan kana jam'iyya mai mulki ko kana kusa da gwamnati, idan ka yi cin hanci babu abin da zai faru.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NSCDC ta kama dan Boko Haram a jihar Adamawa

Ya ce shugaba Buhari ya nuna wa 'yan Najeriya cewa ko da dansa ko amininsa ne ya kauce wa hanya ta fuskar cin hanci da rashawa zai yi maganinsa.

A baya dai, NAIJ.com rahoto cewa majalisar dattijan Najeriya ta bukaci shugaba Buhari ya dauki mataki a kan sakataren gwamnatin nasa, amma sai bangaren zartarwar ya yi biris.

Har ma ya aika da wata takarda da ke nuna cewa Babachir Lawal ba shi da wani laifi kuma gwamnati ta wanke shi daga zargin da aka yi masa.

Shehu Sani ya ce da sun fito da rahoto na biyu, da an ga munin kazantar da aka aikata.

A cewarsa sun tuntubi Babban Bankin Najeriya wanda ya ba su bayanai da asusun ajiyar da aka sanya irin wadannan kuɗaɗe.

Sanata Shehu Sani ya ce a baya, ya zargi bangaren zartarwa da nuna son kai a yakin da cin hanci saboda a cewarsa wasu jami'an gwamnati sun fitar da takardar da ke wanke Babachir Lawal.

"Lokacin da shugaban kasa bai nan, su jami'an gwamnati da ke kusa da shi, sai suka je suka rubuto takarda da sunansa suka ce wadanda suka saci wadannan kudi, suka kau da wadannan kudi cewa wai ya riga ya wanke su."

"Abin da ni kuma na ce ba gaskiya ba ne. Kuma da na fadi haka, ga shi magana ta fito fili Buhari bai yarda da wannan takarda da aka rubuta ba. Shi ya sa ya dauki wannan mataki," in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Dangote ya sayar da kamfanin sarrafa Noodles

Shehu Sani ya ce matakin ya aika da wani sako na cewa duk wani jami'in gwamnatin da ya kauce hanya, za a yi maganinsa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Jami'in jam'iyyar APC ya bayyana dalilin da zai sa jam'iyyar sa shan kaye a zaben 2019.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel