Lokuta 4 da Sule Lamido yayi tsokaci kan gwamnatin Shugaba Buhari

Lokuta 4 da Sule Lamido yayi tsokaci kan gwamnatin Shugaba Buhari

- Bayan da Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo ya bayyana tababa a kan yakin da gwamnatin Muhammadu Buhari ke cewa tana yi da cin hanci da rashawa

- Ya kuma ce batun duk hira ce, don kuwa shi ma jagoran gwamnatin yana da tabon rashawa lokacin da ya yi aiki a gwamnatin Janar Sani Abacha

NAIJ.com ta tattaro maku abubuwa hudu da Malam Sule Lamido ya fada akan gwamnatin Buhari.

1. Batun cin hanci da rashawa duk hira ce, don kuwa shi ma jagoran gwamnatin yana da tabon rashawa lokacin da ya yi aiki a gwamnatin Janar Sani Abacha. A wancan lokacin dai ya yi aiki da Abacha. Kuma shi ne na kusa-kusa da shi. In rashawa ce, me ake faɗa kansa a sannan?

2. Abubuwan da ake faɗa kan batun tsaro da rashawa, ina ganin gaskiyar maganar ita ce (Shugaba Muhammadu Buhari) yana yi ne a kan matsayin hira. Ba don gaskiya ba.

Lokuta 4 da Sule Lamido yayi tsokaci kan gwamnatin Shugaba Buhari

Lokuta 4 da Sule Lamido yayi tsokaci kan gwamnatin Shugaba Buhari

3. Akwai rainin hankali a cewa hukumar EFCC ta je wani gida a Legas ta binciko kuɗi. Shin wa ya ba ta labarin wannan gidan? Ai akwai shi! Kuma mai ba da labarin wa ya ce ya mallaki kuɗin?

Ya ce zancen kawai ne a ce hukumar leƙen asiri ta ƙasa NIA ta rasa inda za ta ajiye kuɗinta sai ta kai su wani gida can a Legas.

KU KARANTA: An kama wani rikakken dn Boko Haram a Sambisa

4. Muddin za ka nemi muƙami a Nijeriya, ka neme shi a kan matsayin hankali, a kan hujjar (gina) ƙasa da yanayin shugabanci a duniya.

Kada yanayin haukan ƙasa ya firgata ka, ka biye masa. kamata yi a ce "muna da ƙarfin zuciya da ƙarfin imanin da ke sa wa, mu tsaya a kan gaskiya, ko da 'ya'yanmu za su ce ba su yarda ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wasu jami'an gwamnati ne da ake zargi da cin hanci da rashawa a kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel