Dangote ya sayar da kamfanin sarrafa Noodles

Dangote ya sayar da kamfanin sarrafa Noodles

- Alhaji Aliko Dangote ya sayar da wata bangaren sarrafa Noodles ga wata kamfanin mai suna Dufil Prima Foods .

- Bangarorin biyu sun cimma wata yarjejeniya da zai sa kamfanin Dufil Prima Foods ta ci gaba da samar da kuma sayar da noodles da sunan 'Dangote Noodles' na tsawon shekaru 2 kafin ta canza sunan.

Kamfanin shahararren dan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote, wato Dangote Flour Mills ta bar kasuwancin sarrafa noodles bayan da suka sayar da kaddarorin ga kamfanin Dufil Prima Foods, masu yin Indomie noodles.

A wata sanarwar kamfanin a ranar Talata,18 ga watan Afrilu, an mika wasu daga cikin bangaren kamfanin ga kamfanin Dufil don yi amfani da su na rikon kwarya, wannan mataki zai taimaka wajen mika bangaren kamfanin.

Kamfanin sarrafa noodles na daga cikin DFM, wanda Dangote ya saya a kwanan nan daga Tiger Brands.

Dangote ya sayar da kamfanin sarrafa Noodles
Dangote ya sayar da kamfanin sarrafa Noodles

Babban manajan kamfanin Dangote Flour Mills, Thabo Mabo, ya ce sayar da bangaren sarrafa Noodles wata dabaru ne na mayar da hankali a kan samar da yankunan gari da kuma taliya, inda kamfanin ke da karfin kasuwanci.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya dakatar da sakataren gwamnati da shugaban hukumar tsaron sirri, NIA

Mabo ya ce, a karkashin yarjejeniya da sharuddan tallace-tallace, kamfanin Dufil Prima Foods, zai ci gaba da samar da kuma sayar da noodles da sunan 'Dangote Noodles' a jikinta na tsawon shekaru 2 kafin ta canza sunan.

Babban jami'in kamfanin Dufil Prima Foods, Deepak Singhal, ya tabbatar da haka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel