Ya kamata EFCC ta gaggauta sanar da masu kudin Ikoyi - Saraki

Ya kamata EFCC ta gaggauta sanar da masu kudin Ikoyi - Saraki

- Majalisar dattawa ta bukaci hukumar kasar EFCC, da ta gaggauta bayyana mamallakan makuden kudaden da yawansu ya kai Dala Miliyan 43

- Saraki ya ce, EFCC ce ke da alhakin kawo karshen cecekucen da ake yi ta hanyar bayyana ainihin mutanen da suka tara makudaden kudaden a cikin gidan na Ikoyi

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC, da ta gaggauta bayyana mamallakan makuden kudaden da yawansu ya kai Dala Miliyan 43, wanda aka gano a wani kasaitaccen gida da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas.

A wata zantawa da ya yi da manema labarai, shugaban Majalisar dattawan Bukola Saraki ya ce, cecekucen da ake ci gaba da yi kan kudaden na dakushe martabar Najeriya.

Mr. Saraki ya ce, EFCC ce ke da alhakin kawo karshen cecekucen da ake yi ta hanyar bayyana ainihin mutanen da suka tara makudaden kudaden a cikin gidan na Ikoyi.

Ya kamata EFCC ta gaggauta sanar da masu kudin Ikoyi - Saraki

Bukola Saraki yace ya kamata EFCC ta gaggauta sanar da masu kudin Ikoyi

NAIJ.com ta rahoto cewa, ko a jiya Talata, sai dai hukumar ta EFCC ta sake samame a gidan, in da a wannan karo ta binciki sassan tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP mai adawa, Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu.

KU KARANTA KUMA: ‘Wanene fadar shugaban kasa?’ – Babachir Lawal ya maida martani ga dakatar da shi

Wannan na zuwa ne bayan wasu jami’an leken asiri sun ce, akwai yiwuwar an boye wasu kudaden daban a sassan gidan.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wata mata dake rokon gwamnati da karda ta rushe mata gida:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel