Abin da ya sa mu ke karbar kudin mazabu-Inji Saraki

Abin da ya sa mu ke karbar kudin mazabu-Inji Saraki

– Bukola Saraki ya kare Majalisa inda yace akwai dalilin karbar kudin mazabu

– Shugaban Majalisar datttawar yace ta haka ne kurum za su yi wa Jama’an su aiki

– Sai dai mafi yawa ba a ganin romon

Abin da ya sa mu ke karbar kudin mazabu-Inji Saraki

Shugaban Majalisa Bukola Saraki

Kwanaki NAIJ.com ta rahoto cewa Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki ya nemi mutanen Najeriya su kara hakuri su kuma cigaba da marawa Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.

Shugaban Majalisar Dattawa ya bayyana dalilin da ya sa ake ba Sanatocin kasar kudi domin gudanar da kwangiloli a mazabun su. Bukola Saraki ya bayyana wannan ne a karshen wancan makon.

KU KARANTA: Saraki yayi magana game da EFCC

Abin da ya sa mu ke karbar kudin mazabu-Inji Saraki

Bukola Saraki

Bukola Saraki ya bayyana wannan ne a lokacin da aka nada sa Baba Addini na Ansar-Deen a Kwara lokacin da ya je hutun Easter da aka yi. Bukola Saraki ya kare Sanatocin duk da cewa ba a ganin wasu ayyukan da ake yi a kasa. Saraki dai yace ta haka ne kurum Jama'a za su ci romon Damukaradiyya.

Saraki yace yana sa rai cewa Jam’iyyar su ta APC za ta cika alkawarun da ta dauka a lokacin yakin neman zabe.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

APC na cikin matsala kenan? Inji Timi Frank

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel