Gwamna El-Rufai da Buratai sun ƙaddamar da ‘Operation Harbin Kunama II’ a kudancin Kaduna

Gwamna El-Rufai da Buratai sun ƙaddamar da ‘Operation Harbin Kunama II’ a kudancin Kaduna

- Gwamnatin jihar Kaduna tare da rundunar sojan kasa sun kaddamar da 'Operation harbin kunama II'

- Gwamna Nasir El-Rufai tare da laftanar janar Buratai sun halarci bikin kaddamarwar

A kokarinta na magance rikita rikitan data dabaibaye kudancin Kaduna, gwamnatin jihar Kaduna tare da hadin gwiwar rundunar sojin kasa ta kaddamar da aikin tsaro na musamman mai taken ‘Operation Harbin Kunama II’.

Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai tare da babban hafsan rundunar mayakan sojan kasa ta kasa laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ne suka kaddamar da aikin a ranar Laraba 19 ga watan Maris a garin Kafanchan.

KU KARANTA: Rundunar Soji ta kai harin samame akan yan ta’addan Boko Haram

A jawabinsa, gwamna El-Rufai yace manufar kaddamar da wannan aiki na musamman shine don kare lafiya tare da dukiyoyin mazuana yankin, da kuma tabbatar da tsaro a jihar gaba daya, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Gwamna El-Rufai da Buratai sun ƙaddamar da ‘Operation Harbin Kunama II’ a kudancin Kaduna

Gwamna El-Rufai yayin ƙaddamar da ‘Operation Harbin Kunama II’

Shima janar Buratai ya nanata muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al’umma, daga nan yayi alwashin dakarun soji zasu yi iya bakin kokarinsu wajen ganin sun ga bayan duk wasu nufin tada zauni tsaye a yankin.

Gwamna El-Rufai da Buratai sun ƙaddamar da ‘Operation Harbin Kunama II’ a kudancin Kaduna

Gwamna El-Rufai da Buratai

Yankin kudancin Kaduna ya sha fama da fadace fadace a tsakanin mazauna yankin da Fulani makiyaya, wanda hakan yayi sanadiyyar salwantar rayuka da dama, don ko a satin data gabata sai da aka kai hari wani kauyen Asso dake garin Jama’a.

Gwamna El-Rufai da Buratai sun ƙaddamar da ‘Operation Harbin Kunama II’ a kudancin Kaduna

Gwamna El-Rufai yana karbar gaisuwa

A baya ma dai gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar rundunar soji sun yi hubbasan samar da barikin sojoji a yanki, sai dai a ranar da suka saka tubakin ginin barikin, sai wasu marasa kishin kasa suka rusa shi. Amma gwamna El-Rufai yace ba zasu fasa gina barikin ba.

Gwamna El-Rufai da Buratai sun ƙaddamar da ‘Operation Harbin Kunama II’ a kudancin Kaduna

Manyan baki a yayin kaddamarwar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon rikicin kudancin Kaduna

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel