‘Wanene fadar shugaban kasa?’ – Babachir Lawal ya maida martani ga dakatar da shi

‘Wanene fadar shugaban kasa?’ – Babachir Lawal ya maida martani ga dakatar da shi

- Babban sakataren gwamnatin tarayya, ya fada ma masu kawo rahoto da su tambayi fadar shugaban kasa dalilin dakatar da shi

- Da aka sanar da shi cewan fadar shugaban ce ta sanar da dakatar da shi, ya amsa da: “Wanene fadar shugaban kasa?”

Babachir Lawal, babban sakataren gwamnatin tarayya, ya fada ma masu kawo rahoto da su tambayi fadar shugaban kasa dalilin dakatar da shi.

Da yayi karo da masu kawo rahoto a ranar Laraba jim kadan bayan an sanar da dakatar da shi, Lawal wanda ke cike da jimami karara ya ja burki a dukkan tambayoyi da akayi masa.

Da aka sanar da shi cewan fadar shugaban ce ta sanar da dakatar da shi, ya amsa da: “Wanene fadar shugaban kasa?”

‘Wanene fadar shugaban kasa?’ – Babachir Lawal ya maida martani ga dakatar da shi

Babachir Lawal ya maida martani ga dakatar da shi da fadar shugaban kasa ta yi

Yana cikin ganawa da mataimakin shugaban kasa lokacin da Femi Adesina, kakakin shugaban kasa, ya sanar da dakatarwan shi har sai an kammala binciken kwangilar da aka bashi karkashin shirin shugaban kasa a kan yan Arewa maso gabas wato Presidential Initiative on the North East (PINE).

Har ila yau an kuma dakatar da Ayo Oke, darakta Janar na hukumar leken asirin Najeriya (NIA), kan kudin da hukumar EFCC ta gano a wani kira a Ikoyi.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Kano ta bayar da damar a maida masallacin Idi kasuwa

NAIJ.com ta tattaro maku yadda ya amsa tambayoyin:

Masu rahoto: An sanar da dakatar da kai. Ta yaya zaka maida martani kan al’amarin? Sai Lawal ya amsa da: Wanene ya sanar?

Masu rahoto: Fadar shugaban kasa.

Lawal: Toh ku tambaye su. Me yasa kuke tambaya na? Wanene fadar shugaban kasa?

Masu rahoto: Shin an sanar da kai batun dakatarwan?

Lawal: Daga wa? Kan me. Ku fa? An sanar da ku?

Masu rahoto: Kwarai.

Lawal: Daga wa?

Masu rahoto: Daga fadar shugaban kasa.

Lawal: Ban gani ba. Da na baku… ban ga sanarwan kafar watsa labarai ba don haka ba zan iya sharhi a kai ba.

Masu rahoto: Yanzu haka yana tashe a yanar gizo. Shin kana tantama a kan gaskiyar sanarwan ne?

Lawal: Ban gani ba"

Masu rahoto: Fada mana sakamakon ganawarka da mataimakin shugaban kasa.

Lawal: A koda yaushe ina nan. Ina ganawa da mataimakin shugaban kasa a koda yaushe. Na saba zuwa nan tun ma kafin a nada ni a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Jami'in jam'iyyar APC ya fadi dalilin da zai sa jam'iyyar sa ta sha kaye a 2019.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel