EFCC: Ministan Buhari ya maka wasu a Kotu

EFCC: Ministan Buhari ya maka wasu a Kotu

– Rotimi Amaechi ya maka Femi Fani-Kayode a Kotu

– Amaechi na bukatar a biya sa sama da Biliyan 1

– An zargi Amaechi da mallakar Dala miliyan 43 a Ikoyi

EFCC: Ministan Buhari ya maka wasu a Kotu

Minista Amaechi ya maka wasu a Kotu

NAIJ.com na da labarin cewa wani tsohon Minista kuma rikakken Dan PDP watau Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa Amaechi ne ya mallaki makudan kudin da Hukumar EFCC ta gano a wani gida a Ikoyi kwanan nan na Jihar.

Tsohon Gwamnan na Jihar Ribas Rotimi Amaechi wanda yanzu Ministan Buhari ne ya kai karar Femi Fani-Kayode da kuma Gwamna Ayo Fayose Kotu inda yace sun masa sharri su na kuma nema su bata masa suna.

KU KARANTA: Buhari bai halarci taron da aka saba ba

EFCC: Ministan Buhari ya maka wasu a Kotu

Ministan sufuri Rotimi Amaechi

Gwamna Nyeson Wike na Jihar Ribas yayi irin wannan ikirari inda yace kudin na Jihar Ribas ne tun lokacin Rotimi Amaechi yana Gwamnan Jihar. Ministan sufurin kasar Rotimi Amaechi ya nemi a biya sa Naira Biliyan 1.25 saboda wannan kasafi da aka yi masa.

Dama Kungiyar SERAP tace ya kamata shugaban kasar ya fitar da Jama’a daga cikin duhu a daina boye-boye kowa ya gane wanda ya mallaki wadannan kudi. Tuni dai yanzu shugaba Buhari ya dakatar da shugaban Hukumar NIA na.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gwamnatin Buhari ta fara bin barayi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel