Ina Buhari ya shige; wannan mako ma ba ayi taro ba

Ina Buhari ya shige; wannan mako ma ba ayi taro ba

– Shugaba Buhari bai halarci taron Majalisar FEC ba kwanaki

– Haka wannan makon ba a zauna ba

– Shugaban kasar ya bayyana dalilin hakan

Ina Buhari ya shige; wannan mako ma ba ayi taro ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a taro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya hana a gudanar da taron mako-mako na Majalisar sa ta zartarwa da aka saba. Garba Shehu yace rashin isasshen lokaci ne ya hana a gudanar da taron.

An dai saba yin wannan taro na Ministoci da sauran Jami’an Gwamnatin a fadar shugaban kasa a kowace Laraba. Sai dai shugaban kasar yace wannan karo an dawo hutun Easter a kurarren lokacin don haka aka bari sai Ministoci sun kintsa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya soke taron yau

Ina Buhari ya shige; wannan mako ma ba ayi taro ba

Shugaban kasa Buhari a fadar Villa

Wancan makon da ya wuce ma dai shugaban kasa bai halarci taro ba inda Mataimakin sa ne ya ja ragamar. Ministan yada labarai yace ba wata matsala ce ta sa hakan ba illa-iyaka shugaban kasar ya ba Farfesa Yemi Osinbajo dama domin shi ya cigaba da wasu ayyuka na dabam.

NAIJ.com na da labari cewa dazu ne dai yanzu shugaba Buhari ya dakatar da shugaban Hukumar NIA na kasa da kuma Sakataren Gwamnatin sa Babachir David Lawal.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Najeriya sun koka da yunkurin rushe masu gidaje

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel