Yaki da cin hancin Najeryia duk hira ce - Sule Lamido

Yaki da cin hancin Najeryia duk hira ce - Sule Lamido

- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana tababa a kan yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatin Buhari

- A cewarsa batun duk hira ce don shi kan sa jagoran gwamnati na da tabon rashawa

- A ganin sa yaki da cin hancin da gwamnatin APC ke yi, ya fi karkata a kan jami'an gwamnatin PDP ne

- Ya bukaci shugabanni su rika fada wa mabiyansu gaskiya, maimakon biye wa son rai a kan rashin gaskiya ba

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana tababa a kan yakin da gwamnatin Muhammadu Buhari ke cewa tana yi na cin hanci da rashawa.

A cewarsa batun duk hira ce, don kuwa shi ma jagoran gwamnatin yana da tabon rashawa lokacin da ya yi aiki a gwamnatin Janar Sani Abacha.

"A wancan lokacin dai ya yi aiki da Abacha. Kuma shi ne na kusa-kusa da shi. In rashawa ce, me ake fada kansa a sannan?"

Yaki da cin hancin Nigeria duk hira ce - Sule Lamido

Sule Lamido ya ce yaki da cin hancin gwamnatin Buhari duk hira ce

Ya ce: "Abubuwan da ake fada kan batun tsaro da rashawa, ina ganin gaskiyar maganar ita ce Shugaba Muhammadu Buhari yana yi ne a kan matsayin hira. Ba don gaskiya ba."

Kusoshin jam'iyyar adawa ta PDP irinsu Lamido na ganin yaki da cin hancin da gwamnatin APC ke yi, ya fi karkata a kan jami'an gwamnatin PDP wadda ta yi shekara 16 tana mulki a kasar.

KU KARFANTA KUMA: Gwamnatin jihar Kano ta bayar da damar a maida masallacin Idi kasuwa

Sule Lamido wanda yake a matsayin beli kan tuhumar cin hanci da hukumar EFCC ke yi masa a gaban kotu, ya ce akwai rainin hankali kan yadda ake cewa an bankado makudan kudi amma ba a san mai su ba.

"Akwai rainin hankali a cewa hukumar EFCC ta je wani gida a Legas ta binciko kudi. Shin wa ya ba ta labarin wannan gidan? Ai akwai shi! Kuma mai ba da labarin wa ya ce ya mallaki kudin?"

Ya ce zancen kawai ne a ce hukumar leken asiri ta kasa NIA ta rasa inda za ta ajiye kudinta sai ta kai su wani gida can a Legas.

Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, ya bukaci shugabanni su rika fada wa mabiyansu gaskiya, maimakon biye wa son rai a kan rashin gaskiya ba.

"Muddin za ka nemi mukami a Najeriya, ka neme shi a kan matsayin hankali, a kan hujjar gina kasa da yanayin shugabanci a duniya.

Kada yanayin haukan kasa ya firgata ka, ka biye masa", in ji Lamido.

A cewarsa kamata yi a ce "muna da karfin zuciya da karfin imanin da ke sa wa, mu tsaya a kan gaskiya, ko da 'ya'yanmu za su ce ba su yarda ba."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Sarki Sanusi ya kalubalanci shugabannin Najeriya:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel