Buhari ya soke taron majalisar zartarwa na yau

Buhari ya soke taron majalisar zartarwa na yau

- Shugaba Muhammadu Buhari ya soke taron majalisar zartarwa na yau Laraba, 19 ga watan Afrilu

- Babu wanda aka gani daga cikin mukarraban gwamnati da aka ga ya halarci dakin da ake gudanar da taron

- Fadar shugaban kasa bat ace komai ba akan batun a lokacin wannan rahoton

Ba’a gudanar da Taron majalisar zartarwa da aka saba gudanarwa a duk mako ba a yau.

Har zuwa karfe 12 saura na safiyar yau, babu wanda aka gani daga cikin mukarraban gwamnati da aka ga ya halarci dakin da ake gudanar da taron.

Kuma har zuwa lokacin wannan rahoton babu wata sanarwa daga fadar shugaban kasa kan dalilin kin gudanar da taron.

Buhari ya soke taron majalisar zartarwa na yau

Buhari ya soke taron majalisar zartarwa na yau

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta bada lissafin jimillan kudin da ta kwato ga shugaba Buhari

Idan ba a mance ba a baya NAIJ.com rahoto cewa sakamakon rashin halartar taron da shugaba Buhari bai yi ba a zaman da aka yi a makon da ya gabata, ya jawo yada jita-jitar cewa shugaban na fama da rashin lafiya, har sai da ta kai ga ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya fito ya karyata batun, inda ya ce shugaban na nan cikin koshin lafiya.

Lai Mohammed ya kara da cewa rashin halartar shugaban kasar ofis ba wai yana nufin ba ya aiki bane.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wani mutumi da yayi barazanar yin sata idan abubuwa basu daidaita ba a kasar:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel