Rundunar Soji ta kai harin samame akan yan ta’addan Boko Haram (Hotuna)

Rundunar Soji ta kai harin samame akan yan ta’addan Boko Haram (Hotuna)

- Dakarun sojan kasa sun kai wani harin ba zata akan yayan kungiyar Boko Haram

- Sojoji sun kashe yan ta'adda guda 6 tare da kwato makamai da alburusai da dama

Dakarun soji na bataliya ta 192 dake gudanar da aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas na ‘OPERATION LAFIYA DOLE’ ta kai wani harin ba-zata kan mafakar yan Boko Haram a ranar Talata 18 ga watan Afrilu da sassafe.

Mayakan rundunar sojin kasan sun kai samamen ne a mafakar yan Boko Haram dake kauyen Dissa da Patawa a jihar Borno.

KU KARANTA: Wasu yan Boko Haram sun hallaka soji 5 a Maiduguri

A yayin harin, sojoji sun samu nasarar kashe yan ta’adda guda 6 tare da jikkata wasu da dama, sa’annan sun kwato makamai da suka hada da bindigar AK-47 guda 1, alburusai da dama, kekuna 3 da buhun gyada 3.

Rundunar Soji ta kai harin samame akan yan ta’addan Boko Haram (Hotuna)

Sojoji suna kona mafakar yan Boko Haram

Bugu da kari sojojin sun gano makudan kudi da suka haura naira dubu ashirin da tara, N29,000 a jikin daya daga cikin yan ta’addan, kamar yadda NAIJ.com ta samu rahoto.

Rundunar Soji ta kai harin samame akan yan ta’addan Boko Haram (Hotuna)

Bindigar da aka kwato

A wani labari makamancin wannan, runduna ta 82 na sojin kasa ta tare wasu mutane dake kai ma yan Boko Haram kayan masarufi a kauyen Daushe a ranar Laraba 19 ga watan Maris, inda aka same su da buhunan dawa.

Daga karshe rundunar sojin kasa ta ceto wata mata mai shekaru 36 a hanyarsu ta dawowa, dakarun rundunar sun smau matar dauke da harbin harsashi.

Ga sauran hotunan:

Rundunar Soji ta kai harin samame akan yan ta’addan Boko Haram (Hotuna)

Sabulai da sauransu

Rundunar Soji ta kai harin samame akan yan ta’addan Boko Haram (Hotuna)

Keken yan Boko Haram

Rundunar Soji ta kai harin samame akan yan ta’addan Boko Haram (Hotuna)

Tarkacen yan Boko Haram

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli barnar da Boko Haram tayi a Borno

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel