Sanata Shehu Sani yayi jimamin rasuwar Ahmadu Chanchangi

Sanata Shehu Sani yayi jimamin rasuwar Ahmadu Chanchangi

- Allah yayi ma hamshakin dan kasuwa Alhaji Ahmadu Chanchangi rasuwa

- Sanata Shehu Sani ya taya al'umman Kaduna jimamin mutuwar Chanchangi

Sanatan mazabar Kaduna ta tsakiya, kwamared Shehu Sani ya bayyana rasuwar hamshakin attajirin nan na Kaduna wato Alhaji Ahmadu Chanchangi a matsayin wani gibi mai wuyar cikewa.

Sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na facebook inda yayi ma iyalan mamacin da sauran jama’a ta’aziyyar rashin Alhaji Ahmadu Chanchangi. Shehu Sani yace;

KU KARANTA:

“Na kadu matuka da samun labarin mutuwan daya daga cikin hamshakan yan kasuwa a Arewa kuma mai taimakon talakawa, Alhaji Ahmadu Chanchangi, wanda gaba daya rayuwarsa ya sadaukar da ita ne a yi ma al’umma hidima, tare da ganin an samar da hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Sanata Shehu Sani yayi jimamin rasuwar Ahmadu Chanchangi

Marigayi Alhaji Ahmadu Chanchangi

“Halayyar Chanchangi na nuni da jajircewar sa wajen taimakon na kasa tare da nuna kauna ga talakawa, mutum ne wanda ya baiwa yayan talakawa daman yin karatu kyauta a makarantansa, ta haka ya kawar da jahilci akan mutane da dama.

“Ba za’a taba mantawa da Chanchangi ba, musamman wadanda suka taba haduwa da shi ko kuma suka karu da shi. Da fatan Allah ya jikan shi da rahama. Amin.” Inji Sanata Shehu Sani.

A ranar laraba 19 ga watan Afrilu ne NAIJ.com ta kawo muku rahoton rasuwar Chanchangi da safiyar ranar bayan ya kwashe tsawon lokaci yana fama da rashin lafiya. Marigayi Chanchangi ya rasu yana da shekaru 86, kuma ya bar mata 3 da yaya 33.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Iyayen yan matan Chibok da dama sun rasu, kalla a nan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel