Buhari ya dakatar da sakataren gwamnati da shugaban hukumar tsaron sirri, NIA

Buhari ya dakatar da sakataren gwamnati da shugaban hukumar tsaron sirri, NIA

- Shugaban kasa ya dakatar da sakataren gwamnatin Babachir daga aiki

- Bugu da kari shugaba Buhari ya dakatar da shugaban hukumar tsaron sirri na NIA, Oke

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a gudanar da bincike cikin badakalar bada kwanagilolin ayyukan jin kai a yankin Arewa maso gabas da ake tuhumar sakataren gwamnati Babachir David Lawal da shi.

Haka zalika shugaban ya sallami sakataren nasa har sai an kammala gudanar da bincikensa. Bugu da kari shugaba Buhari ya bada umarnin a gudanar da cikakken bincike kan makudan kudaden da aka bankado a wani katafren gida dake jihar Legas, wanda hukumar tsaron sirri ta NIA tayi ikirarin cewa nata ne.

KU KARANTA: Mai martaba Sarkin Gombe ya sanya marayu 3,000 a makaranta

Binciken da Buhari ya bada umarnin a gudanar ya hada da gano yadda NIA ta mallaki wadannan makudan kudade, ta yaya, way a basu da kuma umarnin waye ya basu kudin, sa’annan shugaba Buhari ya bukaci a gano an karya doka a hakan ko kuwa?

Buhari ya dakatar da sakataren gwamnati da shugaban hukumar tsaron sirri, NIA

Babachir David Lawal

Shima a nan NAIJ.com ta ruwaito Buhari ya bada umarnin dakatar da shugaban NIA, Ambassador Ayo Oke, har sai yadda halin binciken ya nuna.

Buhari ya dakatar da sakataren gwamnati da shugaban hukumar tsaron sirri, NIA

Shugaban hukumar tsaron sirri, NIA, Jakada Oke

Saboda haka shugaban Buhari ya kaddamar da kwamitin mutum uku data kunshi Lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, mashawarcin shugaban kasa a bangaren tsaro, Munguno da kuma mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo a matsayin shugaban kwmatin.

Shugaba Buhari ya ba kwamitin sati biyu su karkare bincikensu tare da mika masa rahoto cikin sati 2, don haka ya umarci babban jami’i na biyu a ofishin sakataren gwamnati da na hukumar NIA dasu dauki ragamar mulki har sai an kammala bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bacin ya sanya wani mutum kiran ya kamata a binne shuwagabanin Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel