Hukumar EFCC ta gaggauta sanar da masu kudin Ikoyi – Inji sanata Saraki

Hukumar EFCC ta gaggauta sanar da masu kudin Ikoyi – Inji sanata Saraki

- Shugaban majaliar dattawan Najeriya, sanata Bukola Saraki ya bukaci hukumar EFCC da ta bayyana mamallakan makuden kudaden da aka gano a wani gida a Legas

- Sanatan ya ce hukumar EFCC kawai ke da alhakin kawo karshen cece-kucen da ake yi ta hanyar bayyana ainihin mutanen da suka tara makudaden kudaden

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC, da ta gaggauta bayyana mamallakan makuden kudaden da yawansu ya kai Dala Miliyan 43, wanda aka gano a wani kasaitaccen gida da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas.

A wata zantawa da ya yi da manema labarai, shugaban majaliar dattawan Bukola Saraki ya ce, cece-kucen da ake ci gaba da yi kan kudaden na dakushe martabar Najeriya. Inji NAIJ.com.

Sanata Saraki ya ce, EFCC ce ke da alhakin kawo karshen cece-kucen da ake yi ta hanyar bayyana ainihin mutanen da suka tara makudaden kudaden a cikin gidan na Ikoyi.

KU KARANTA KUMA: Karin labaru game da babbar hasumiyai Osborne da EFCC suka caje dakuna wani tsohon gwamnan

Rohatanni sun ce, ko a jiya Talata, sai dai hukumar ta EFCC ta sake samame a gidan, inda a wannan karo ta binciki sassan tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP mai adawa, Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu.

Wannan na zuwa ne bayan wasu jami’an leken asiri sun ce, akwai yiwuwar an boye wasu kudaden daban a sassan gidan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC
NAIJ.com
Mailfire view pixel