Gwamnonin arewa na shirin daukan mataki akan Sarkin Kano

Gwamnonin arewa na shirin daukan mataki akan Sarkin Kano

-Wasu gwamnoni na kokarin cin mutuncin Sarkin Kano

-Sun lashi takobin taka masa burki a wannan kasa

Aƙalla Gwamnonin arewacin Najeriya 6 ciki sun hadu a ƙasar Sin, inda suka yi yarjejeniyar daukar mataki akan Sarkin Kano.

Zaman taron da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya jagoranta sun cimma matsaya bayan doguwar muhawara a Ritz Carlton Hotel ranar Lahadi da ta gabata.

Majiya ta bada rahoton cewa, wasu gwamnonin suka goyi bayan cire Sarki Sanusi II yayin da wasu gwamnoni biyu suka goyi bayan a binciki kuɗaɗen asusun Masarautar Kano da wasu suka yi zargin Sarkin yaci.

Gwamnonin sun amince cewa matukar aka bar Sarki Sanusi II a kujerarsa ba tare da daukar mataki akan sa ba, zai cigaba da cin mutuncinsu. Don haka a kawar da shi a kawo wani da talakawan jihar Kano zasu amince da shi.

Gwamnonin da suka halarci zaman sun hada da Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje; Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari; Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal; Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello; Gwamnan jihar Nassarawa, Tanko Almakura da kuma Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu

Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu

Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu
NAIJ.com
Mailfire view pixel