Wasu yan Boko Haram sun hallaka soji 5 a Maiduguri

Wasu yan Boko Haram sun hallaka soji 5 a Maiduguri

-An hallaka jami’ an sojin Najeriya 4 a jihar Borno

- Ana zargin cewa mayakan Boko Haram ne sukayi wannan aika-aika

Wasu yan tada kayan bayan Boko Haram sun hallaka sojin Najeriya 5 kuma sun jikkata wasu 5 a mazaunin soji a yankin arewa maso gabashin kasa.

Wani jami’in soja ya bayyanawa manema labrai a ranan Talata cewa : “Sun zo da yawa kuma sun fimu yawa da bindiga."

Yan Boko Haram din wadanda ke karkashin Abu Musab Al-Barnawi sun afka mazaunin jami’an soji da ke kusa Sabon garin Kimba kimannin kilomita 140 daga Maiduguri.

Wasu yan Boko Haram sun hallaka soji 5 a Maiduguri

Wasu yan Boko Haram sun hallaka soji 5 a Maiduguri

Mustapha Karimbe, wani mai taimakawa soji yace yan Boko Haram din sun zo cikin motocin soji kuma sun kona motocin soji 3.

" Yan ta’addan sun afkawa soji…. Kuma sun kasance a kauyan na awa 3 kafin suka wuce”

KU KARANTA: Sarkin Gombe ya sa marayu 3000 a makaranta

Wannan shine karo na biyu da za’a kai hari wannan mazaunin sojin cikin wata 1.

A wata jiya, yan Boko Haram din sanye da kayan soji sun kai hari wurin inda suka kora sojin kuma suka saci abinci da magunguna a kauyen.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel