Kasar Amurka fa ta rude jama'a, ana gudanar da zanga zangar kin jinin Trump

Kasar Amurka fa ta rude jama'a, ana gudanar da zanga zangar kin jinin Trump

- Fiye da shekaru arba'in shugabannin da suka mulki Amurka kan nuna takardun su na haraji a fili

- Mutane da dama a Amurka da ke na kalubalantar shugaban kasa Donald Trump

Inda suke cewa ya kamata ya bayyana takardun sa na haraji a fili kamar yadda kowanne shugaban kasar Amurka ya yi fiye da shekaru arba’in a baya.

Mutane da dama sun yi zanga zanga da suka yi wa lakabi da “Tattakin Haraji” a birane fiye da 100 a fadin Amurka, domin nuna rashin jin dadin su bisa kin bayyana takardun harajin da shugaban yaki, inda suke cewa sai dai na boye wani abu ne da ba ya son a gani.

NAIJ.com tasa mu labarain cewa Trump ya yi kwana daga katafaren Mar-a-Lago dake Forida da alamun baya son haduwa da masu zanga zangar a West Palm Beach.

Kasar Amurka fa ta rude jama'a, ana gudanar da zanga zangar kin jinin Trump

Kasar Amurka fa ta rude jama'a, ana gudanar da zanga zangar kin jinin Trump

Biranen da masu zanga zangar suka hadu sun hada da Washington, da Philadelphia da Chicago da kuma New York. An tsare mutane da yawa a Berkeley dake jihar California a yayin da masu zanga zanga biyu dake adawa da juna suka hadu suka fara jefa kwalabe da gami da naushin juna.

KU KARANTA: Kaji abin da Saraki ya fada game da Buhari?

Tun da Trump ya shiga ofish a watan Janairu, ya fadawa 'yan jaridu cewa mutanen Amurka basu damu ba idan ya bayyana takardunsa na haraji ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyo game da shugaban kasar Amurka Donald Trump

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel