Gwamnati ta kori dan sandan da aka kama da lalata a bakin aikin sa

Gwamnati ta kori dan sandan da aka kama da lalata a bakin aikin sa

- An sallami wani ɗan sanda daga aiki saboda yin lalata da mata sau da dama a bakin aikinsa tsawon shekara biyu cikin yankin Devon da Cornwall a Ingila

- Ɗan sanda wanda ba a bayyana sunansa ba, ya aikata baɗala da mata biyu waɗanda ya gamu da su lokacin da yake bakin aiki da ofishin 'yan sandan shiyyar Devon da na Cornwall

An gudanar da zaman sauraron wannan bahasi cikin sirri a shalkwatar 'yan sanda ta Exeter makon jiya.

Zaman sauraron ya ji yadda ɗan sandan a wani lokaci ya haike wa wata mata da ke cikin halin ni-'ya-su a bakin aikinsa.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Ya kuma taba fitar da bayanan sirrin hukuma, don haka aka sallame sa kan aikata ba daidai da kuma cin amana.

Gwamnati ta kori dan sandan da aka kama da lalata a bakin aikin sa

Gwamnati ta kori dan sandan da aka kama da lalata a bakin aikin sa

Ayarin jami'an zaman sauraron ya samu ɗan sandan "da keta ƙa'idojin aikin ɗan sanda,'' musammam waɗanda suka jiɓanci tsare sirri, haƙƙoƙi da nauye-nauye, oda da umarni, tsare gaskiya da ƙimar aiki.

KU KARANTA: Shehu Sani ya caccaki Gwamna El-rufai

Wata sanarwa ta ce: "Jami'in ya gaza kiyaye nauye-nauyen da ke kansa a shekara ta 2012 zuwa 2014, a lokuta da dama ta hanyar aikata lalata a bakin aiki, ciki har da saduwa da wata shaida da ke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi."

An sallami wani ɗan sandan ma wata biyar da ya wuce saboda yin lalata da wata mata.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai wata baturiya ce mai yin fenti a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel