Champions league: An yi waje Bayern Munich da Leicester

Champions league: An yi waje Bayern Munich da Leicester

– Real Madrid ta kara ba Kungiyar Bayern Munich kashi

– A zagaye na biyu an tashi 4-2 a gidan Madrid

– Cristiano Ronaldo ya kara jefa kwallaye 3

Champions league: An yi waje Bayern Munich da Leicester

Champions league: Wasu sun ce Alkalin wasa ya cuci Bayern Munich

A bangaren wasanni NAIJ.com na da labari cewa Zakaru Real Madrid sun yi waje da Kungiyar Bayern Munich ta Kasar Jamus daga Gasar UEFA Champions league na zakarun Nahiyar Turai a wasan jiya Talata.

A wasan farko kuna da labari cewa Real Madrid ta doke Bayern Munich da ci 1-2 a gasar. Haka wannan karo Real Madrid ta kara ba Kungiyar Bayern Munich kashi a wasan zagaye na biyu inda aka tashi 4-2 a gidan Santiago na Madrid.

KU KARANTA: Real Madrid ta doke Bayern Munich

Champions league: An yi waje Bayern Munich da Leicester

Lewandowski ya ci wa Bayern Munich mai 'ya 'ya

Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya jefa kwallaye 3 duk shi kadai a wasan inda ya zama dan wasan farko da ya zura kwallaye 100 a Gasar UEFA Champions league. Sai dai Jama’a sun yi korafi game da yadda Alkali ya busa wasan.

Har wa yau Atletico Madrid ta doke Leicester City ta Ingila inda tayi waje a Gasar. Haka kuma yau za a fafata tsakanin Juventus da Kungiyar Barcelona. Dama wancan makon Monaco ta ba Dortmund kashi a Jamus.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Efa yayi nasara a wasan Big Brothe

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel