Gwamnatin jihar Kano ta bayar da damar a maida masallacin Idi kasuwa

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da damar a maida masallacin Idi kasuwa

- Wasu malaman addinin musulunci a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya sun koka kan yadda gwamnatin jihar ta ba da damar gina shaguna a babban masallacin idi na birni.

- Malaman sun nuna damuwa ne kan barazanar da suka ce masallacin Idin na Kano mai tsohon tarihi ke fukanta, ta hanyar mayar da shi wajen kasuwanci.

A cewar malaman hakan bai dace ba, don kuwa babban kuskure ne zaftare wannan wajen ibada mai tsohon tarihi maimakon bunƙasa shi.

Masallacin idin wanda ya yi iyaka da ƙofar mata da Fagge, yana kuma fuskantar barazana daga manyan kasuwannin Kantin kwari da Ƙofar wambai waɗanda suka sanya shi a tsakiya.

NAIJ.com ta tsinkayi sadda Sheikh Abba Adamu ya ce ''Kasuwa ko ina take muna murna da ita, amma filin Idi a rage shi don gina shaguna bai dace ba, babban kuskure ne.''

A yanzu haka, ana amfani da makeken filin wajen ajiye motoci da kuma a matsayin tasha, inda gwamnati ke karɓar haraji daga masu motocin haya da ke ɗaukar kayan 'yan kasuwa.

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da damar a maida masallacin Idi kasuwa

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da damar a maida masallacin Idi kasuwa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a nasa ɓangare cewa ya yi masallacin idi na birnin Kano ya shafe sama da shekara 200 don haka bai kamata gwamnati ta yi wani tunani na rage shi ba.

KU KARANTA: Tsagerun Neja Delta sun ce a binciki Jonathan

Ya ce: "Wannan fili ne mai tarihi, kuma babbar alama ce ta addinin musulunci a jihar Kano, rage shi bai dace ba ko kadan."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wani shon malamin kirista ne da ya musulunta

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel