Zanga-zangar kin jinin ‘yan majalisun dattawan Najeriya

Zanga-zangar kin jinin ‘yan majalisun dattawan Najeriya

- Matasa masu goyon bayan jam’iyyar APC a jihar Neja sun mamaye ofishin sanata David Umaru wanda ke Minna domin nuna bakin cikin su ga dan majalisar game da irin wakilcin da ‘yan majalisun ke yi musu

- Matasan sun ce matakin da za su ‘dauka nan gaba shine shirya yadda za su fara kiranyen ‘yan majalisun da suka zaba su wakilce su

Daruruwan matasa masu goyon bayan jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu ga ‘yan majalisun dattawan Najeriya, akan zaman doya da manja dake tsakaninsu da fadar shugaban ‘kasar Najeriya.

Masu zanga-zangar sun mamaye ofishin shugaban kwamitin shari’a na majalisar dattawan sanata David Umaru, dake Minna fadar gwamnatin jihar Neja. Inda suka bayyana cewa sun taru ne domin nuna bacin ran su ga ‘yan majalisar.

Shugaban tawagar matasan kwamrad Nuraddeen Iliyasu, ya ce sun taru ne domin nuna fushinsu da kuma bacin ran su game da irin wakilcin da ‘yan majalisun su ke yi musu.

Matasan dai sunce matakin da za su ‘dauka nan gaba shine shirya yadda za su fara kiranyen ‘yan majalisun da suka zaba su wakilce su, su kuma sake zaben wasu shugabannin da suke ganin za su yi musu wakilci na gari.

KU KARANTA KUMA: Ba zan ba Saraki hakuri ba don ya maida ni – Inji Ali Ndume

NAIJ.com ta ruwaito cewa, daga baya sanata David Umaru ya kira taron manema labarai domin mayar da martani, inda ya ce su kam suna tare da shugaban kasa Mohammadu Buhari dari bisa dari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon da wani dan jam'iyyar APC ke bayyana nadamar kasancewa a cikin jam'iyyar saboda masaloli daban-daban da ke fuskanta a hannun 'yan jam'iyyar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel