Najeriya ta fita daga cikin matsin tattalin arziki

Najeriya ta fita daga cikin matsin tattalin arziki

– An yi ta, ta kare: Najeriya ta fita daga matsin tattali

– Najeriya tayi kusan shekara guda cikin matsalar tattali

– Watau abin da ake kira 'Recession' idan aka samu dankwafewar tattali

Najeriya ta fita daga cikin matsin tattalin arziki

Allah yayi: Najeriya ta fita daga matsalar tattali

Tun a wani nazari da Jaridar nan ta World Economist tayi aka bayyana cewa Najeriya ta fara fita daga matsalar tattalin arziki a watan jiya. Yanzu dai an tabbatar da cewa kasar ta fita daga matsalar da ta samu na dakushewar tattali.

Jaridar World Economist da ke Landan tace Najeriya ta fito daga kangin matsin da ta samu na tattali haka kuma Hukumar tara bincike da alkaluman kasa watau NBS ta tabbatar da wannan rahoto. Hasashe na nuna cewa harkar kasuwanci yayi dagawar da bai taba yi ba tun bara.

KU KARANTA: Shugaban Majalisa yayi kira a marawa Buhari baya

Najeriya ta fita daga cikin matsin tattalin arziki

Shugaba Buhari da Mataimakin sa Osinbajo

Tattalin Najeriya ya fara mikewa bayan kusan shekara guda yana dakushewa. Ko dai tattalin arzikin kasar bai wani habaka ba amma kasuwanci ya fara mikewa sarai daga wannan wata. Hakanan kuma alkaluman tsadar kaya sun yi kasa.

Kwanaki NAIJ.com ta kawo maku labari daga Hukumar NBS ta kasa cewa farashin kaya sun fara yin kasa a Najeriya. Farashin kaya sun sauka kasa da kashi 0.52% watau cikin kashi dari a wannan wata.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gari yayi wa wani Bawan Allah zafi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel