Za'a gina kamfanin samar da hasken wutar lantarki mai amfani da bola a Arewa

Za'a gina kamfanin samar da hasken wutar lantarki mai amfani da bola a Arewa

- Gwamnatin Kano da babban kamfanin samar da hasken wutar lantarki na kasar China zasu hada hannu domin kafa tashar samar da wutar lantarki daga Bola a Kano

- Kamfanin mai suna Everbright International Boluo Garbage Power Plant, ya shara wajen sarrafa bola zuwa hasken wutar lantarki da za a iya amfani dashi a gidaje da kamfanoni.

Daraktan yada labarai da sadarwa na fadar Gwamnatin Kano, Salihu Tanko Yakasai yace an cimma yarjejeniyar ce a lokacinda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kaiwa kamfanin ziyara a kasar China.

Yace kamfanin na bukatar bola da yawanta yakai ton 800 a kullum domin samar da hasken wutar lantarki. Kuma jihar Kano na samar da kimanin ton 1700 a duk rana.

Kamfanin ya nuna amincewarsa na yin hadaka da jihar domin kafa tashar wutar lantarki a jihar da zai lashe fiye da dala miliyan $250.

Za'a gina kamfanin samar da hasken wutar lantarki mai amfani da bola a Arewa

Za'a gina kamfanin samar da hasken wutar lantarki mai amfani da bola a Arewa

NAIJ.com ta tattaro cewa Gwamna Ganduje ya nuna jin dadinsa da gamsuwarsa game da wannan yunkuri yana mai gayyatar kamfanin da su ziyarci jihar domin fara gudanar da aikin samar da wutar.

KU KARANTA: Barazanar yunwa na karuwa a Najeriya

Everbright dai shine kamfani na farko dake da wannan fasaha ta samar da hasken wuta daga bola kuma wannan shine karo na farko da kamfanin zai kafa rukuni a wajen kasar China.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai sarkin Kano din ne ke magana game da shugabanni

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel