To fa! Gwamnonin arewa sun amince da tsige Sarkin Kano

To fa! Gwamnonin arewa sun amince da tsige Sarkin Kano

- A kalla gwamnonin Arewa shida ciki har da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje sun hadu a Guangzhou, a ƙasar Chana

- Gwamnonin sun cimma yarjejeniyar daukar “mummunan mataki” akan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Zaman taron da shugaban Inuwar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya jagoranta sun cimma matsaya bayan doguwar muhawara a Ritz Carlton Hotel ranar Lahadi da ta gabata.

Majiyar mu ta ruwaito cewa, nan take wasu gwamnonin suka goyi bayan cire Sarki Sanusi II yayin da wasu gwamnoni biyu suka goyi bayan a Binciki kuɗaɗen asusun Masarautar Kano da wasu suka yi zargin Sarkin ya yi Wadaƙa da su.

NAIJ.com ta samu labarin cewa gwamnonin sun amince cewa matukar aka ƙyale Sarki Sanusi II haka siddan ba tare da daukar mataki akan sa ba zai ci gaba da ragargarzar gwamnonin.

To fa! Gwamnonin arewa sun amince da tsige Sarkin Kano

To fa! Gwamnonin arewa sun amince da tsige Sarkin Kano

Don haka a kawar da shi a kawo wanda zai karbu a wajen talakawan jihar Kano.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun kama matar kwamandan Boko Haram

Ana dai zargin gwamnonin da suka halarci zaman sun hada da gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Neja Abubakar Bello, gwamnan jihar Nassarawa Tanko Almakura da kuma gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli yada Sarki Sanusi yake yin kaca kaca da shugabannin arewa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel