Tsagerun Neja-Delta suna bayan Majalisa ta binciki Goodluck Jonathan

Tsagerun Neja-Delta suna bayan Majalisa ta binciki Goodluck Jonathan

– Kuna da labari ana zargin tsohon shugaban kasa Jonathan da lashe wasu makudan kudin rijiyoyin mai

– Kungiyar MEND sun goyi bayan Majalisa ta gurfanar da Jonathan a gaban ta

– Jomo Gbomo na Kungiyar MEND din ya bayyana haka

Tsagerun Neja-Delta suna bayan Majalisa ta binciki Goodluck Jonathan

'Yan Neja-Delta sun ce a binciki Goodluck Jonathan

Kwanaki NAIJ.com ta kawo maku rahoto cewa ana zargin cewa tsohon shugaban kasa Jonathan ya tashi da sama da Dala Miliyan $200 daga cikin kasuwancin Dala Biliyan $1.3 na wani rijiyar mai da aka saida na kasar ba tare da ka’ida ba.

Dama can Majalisar Wakilai ta zauna game da batun inda ake tunani za ta kira tsohon shugaban Jonathan ya gurfana a gaban ta. Wata kungiyar mai suna MEND ta Neja-Delta tace ta goyi bayan dai ayi hakan.

KU KARANTA: A kara hakuri da Buhari Inji Bukola Saraki

Tsagerun Neja-Delta suna bayan Majalisa ta binciki Goodluck Jonathan

'Yan MEND na Neja-Delta sun goyi-bayan yunkurin Majalisa

Mai magana da bakin Kungiyar MEND din Jomo Gbomo yace suna goyon bayan adalci don haka ba su ki a binciki Jonathan ba. MEND tace Jonathan din ya batawa Kasar Najeriya suna a gida da waje.

Haka nan kuma kungiyar MEND ta yi kul da yunkurin tashi da Kamanin Shell na mai daga Jihar Ribas zuwa Legas. Shi dai Goodluck Jonathan ya musanya cewa ya karbi cin hanci wajen saida rijiyoyin man lokacin yana mulki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda ake kai hari ga 'Yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel