Rundunar yan sandan Najeriya zata dauki ma'aikata 30,000 kafin karshen wannan shekarar

Rundunar yan sandan Najeriya zata dauki ma'aikata 30,000 kafin karshen wannan shekarar

- Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa za ta dauki sabbin ma'aikatan Yan-sanda dubu talatin, a duk fadin kasar nan domin, domin samar da kyakkyawan tsaro a kasar

- Mataimakin shugaban yan-sanda na kasa mai kula da shiyar Arewa maso yamman Maigari A Dikko, shi ne ya bayyana haka a lokacin da yakai wa gwamnan Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ziyara a fadar gwamnatin jihar dake Birnin Kebbi.

Ya kuma ce tuni shirin gina gidaje 500 na yan sanda a duk fadin kasar nan ya kusa kankama domin magance matsalolin matsugunan yan sanda.

NAIJ.com ta samu labarin cewa mataimakin Shugaban yan sanda ya ce hukumar yan sandan tuni ta tura takardar neman amincewa da daukar sabbin yan sanda a fadar shugaban kasa kuma da an sanyawa takardar hannu za su sanar da daukar sabbin ma'aikatan.

Saboda hakan, rashin aiki zata raguwa tsakani matasan Najeriya.

Rundunar yan sandan Najeriya

Rundunar yan sandan Najeriya

A jawabin nasa gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya jinjina wa rundunar yan sanda akan kokarinta na tabbatar da tsaro a duk fadin kasar nan.

KU KARANTA: An bayyana rikicin Shugaba Buhari da Majalisa a matsayin wanda bai karewa

Gwamnan ya kuma tabbatar wa Mataimakin Shugaban Yan-sanda cewa jihar Kebbi za ta yi iya kokarin ta wajen bada gudunmuwarta domin tabbatar da tsaro.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai matasane ke murnar dawowar shugaba Buhari a Daura

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel