Gwamnatin Buhari ta ce za a iya kwashe shekaru kafin a kubutar da ‘yan matan Chibok

Gwamnatin Buhari ta ce za a iya kwashe shekaru kafin a kubutar da ‘yan matan Chibok

- Ministan tsaron Najeriya ya ba da kashedin cewar mai yiwu wa a kwashe wasu shekaru kafin a kubutar da ‘yan matan Chibok da yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su

- Da yake zantawa da majiyar mu, Janar Manir Dan Ali mai ritaya, ya ce sojojin suna kutsawa a inda mayakan Boko Haram suka boye a cikin dajin Sambisa wanda girmansa ya mamaye wasu sassan jihohi uku a Arewa maso gabashin Najeriya

Ya ce ya dauki lokaci mai tsawon gaske kafin Amurka ta gano Osama Bin Laden wanda ya shirya harin ranar tara ga watan Satumbar shekarar 2001.

NAIJ.com ta samu labarin yace Amurka ta kwashe shekaru takwas zuwa goma kafin ta gano Bin Laden.

A cewar Dan Ali suna ci gaba da yakin da suke yi a dajin Sambisa a kowane lungu na cikin dajin.

Janar Dan Ali, ya zanta da Muryar Amurka a daidai lokacin da masu fafutukar ganin an kwato 'yan matan suke bukin cika shekaru uku da yin garkuwa da 'yan matan.

yan matan Chibok

yan matan Chibok

Kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da dalibai mata 276 na makarantar sakandaren garin Chibok dake Arewa maso gabashin kasar a ranar 14 ga watan Afirilun 2014.

KU KARANTA: Yan sanda sun tarwatsa magoya bayan Zakzaky

Ya zuwa yanzu ba a gano 195 a cikin 'yan matan ba.

Duk da irin nasarori da aka samu a yaki da Boko Haram, gazawar gwamnatin wurin kwato ko gano inda 'yan matan suke, ya dusashe nasarorin da sojojin suke samu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wani jirgin yaki ne na sojin Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel