Mai martaba Sarkin Gombe ya sanya marayu 3,000 a makaranta

Mai martaba Sarkin Gombe ya sanya marayu 3,000 a makaranta

- Sarkin Gombe Alhaji Abubakar III ya taimaka ma marayu 3000 da tallafin karatu

- Gidauniyar Sarki Abubakar ta fara ne da daukan nauyin marayu 1500

Mai martaba Sarkin Gombe Abubakar Shehu Abubakar lll, ya zama gatan marayu da marasa galibu ta hanyar sanya yara 3,000 a makarantar firamari domin karfafa musu gwiwa su samu ilimi, inji rahoton jaridar Rariya.

NAIJ.com ta ruwaito a cigaba da kokarinsa na kyautata ma jama’arsa, mai martaba ya sake daukan nauyin karatun marayu 1500, wanda haka ya kai yawan wadanda suka samu tagomashinsa zuwa 3000 a karkashin gidauniyar sat a Shehu Usman Abubakar.

KU KARANTA: Jin ra’ayin raba gardama: Buhari ya taya al’ummar ƙasar Turkiyya murna

Yayin da Sarkin ke mikama yaran da suka amfana da wannan tagomashin kayayyakin karatu a fadarsa, Sarki yace dalilin taimaka ma yaran shine rage musu radadin maraici bayan sun rasa iyayensu.

Mai martaba Sarkin Gombe ya sanya marayu 3,000 a makaranta

Sarkin Gombe tare da marayu

Daga nan sai Sarkin ya bukaci masu hannu da shuni da su dinga taimaka ma marasa karfi daga cikin al’umma, musamman marayu da nakasassu.

Mai martaba Sarkin Gombe ya sanya marayu 3,000 a makaranta

Sarki tare da marayu

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Iyayen yan matan Chibok sun kuka, kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel