An kama wani ɗan Najeriya dake yi ma bankunan Amurka fashi da makami

An kama wani ɗan Najeriya dake yi ma bankunan Amurka fashi da makami

- Wani dan Najeriya daya kware wajen yin fashi da makami a kasar Amurka ya shiga hannu

- Dan fashin mai suna Shuaibu Abdullahi ma'aikacin majalisar dinkin duniya ne

Wani ma’aikacin majalisar dinkin duniya, UN, dan Najeriya, Shuaibu Abdullahi ya shiga hannu a ranar Litinin 17 ga watan Afrilu sakamakon kama shi da aka yi da laifin fashi da makami a bankuna hudu na kasar Amurka.

A yanzu haka an gurfanar da Shuaibu mai shekaru 53 gaban kotu inda ake tuhumarsa da aikata fashi da makami tare da kokarin yin fashin, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta shaida mana.

KU KARANTA: Jin ra’ayin raba gardama: Buhari ya taya al’ummar ƙasar Turkiyya murna

Shuaibu yana aikata aika aikan ne a yayin da ake bashi hutun cin abincin rana daga ofishin UN, a wannan lokutta ne yake zakkewa bankunan, inda yake yi musu fashi. Hukumomin sun gano Shuaibi yayi fashin sa na farko ne a ranar 27 ga watan Feburairu, inda ya shiga bankin Santander, inda ya bukaci jami’in bankin daya bashi kudin hannunsa ko ya kashe shi.

An kama wani ɗan Najeriya dake yi ma bankunan Amurka fashi da makami

Shuaibu Abdullahi

Dayake yaji dadin yadda fashinsa na farko ya kasance, Shuaibu sai ya tafi wani banki mai suna Bank of America don sake maimaita halin beran, amma bai samu nasara ba. Amma daga bisani duk a cikin watan Maris, sai ya koma wani reshe na daban na bankin Santander, inda ya kara yi musu fashin kudi.

An kama wani ɗan Najeriya dake yi ma bankunan Amurka fashi da makami

Yayin da yansanda suka kama barawon

A ranar litinin data gabata ne Shuaibu ya shiga bankin HSBC inda ya mika ma jami’in bankin wata karamar takarda, sai dai jami’in bai karanta ba, sai ya bukaci ya nuna mai wata shaida, daga nan sai Shuaibu ya nuna mai yana dauke da bindiga.

Bayan dawowarsa daga aiki ne, sai yansanda suka yi ma Shuaibu tarkon rago, inda suka kama shi bayan wani dansanda dake aiki a UN ya gane shi daga hoton kyamara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani dan Najeriya ya gargadi gwamnati cewar zai rungumi sana'ar sata fa!

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel