Na kirkiro ma'aikata ta musanman domin ci gaban matasa - Inji Honorabul Samaila Suleiman

Na kirkiro ma'aikata ta musanman domin ci gaban matasa - Inji Honorabul Samaila Suleiman

- Honorabul Samaila Suleiman ya ce, kishin matasa ne ya sa ya gabatar da kudurin kirkiro ma'aikata ta musanman domin ci gaban matasan Najeriya

- Samaila ya ce wannan kudurin zai inganta rayuwar matasa da kuma iyaye maza da mata da sauran jama'ar kasa

- Honorabul Samaila ya jinjinawa takwarorinshi na majalisa sakamakon goyan baya da suka baiwa kudurin

Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar karamar hukumar Kaduna ta Arewa Alhaji Samaila Suleiman, ya bayyana cewar kishin matasan yankin mazabarshi da yake yi da kuma sauran matasan Najeriya ya sanya shi gabatar da kuduri a gaban Majalisa yadda Za'a samar da wata ma 'aikata ta musanman domin ci gaban kasa baki daya.

NAIJ.COM ta ruwaito cewa dan majalisar ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Kaduna, inda ya tabbatar da cewar matukar burinshi ya cika an amince da wannan kuduri da ya gabatar, wanda a halin yanzu kudurin ya tsallake bita ta biyu, zai kasance yafi kowa farin ciki da hakan.

Samaila Suleiman wanda matashi ne dan shekaru 34 da haihuwa ya kara da cewar, masana sun bayyana cewar matasa sune kashi 60 cikin 100 na kowace al 'umma, sannan mazabarshi ta Kaduna ta Arewa, mazaba ce wacce ta tara matasa da dama.

KU KARANTA KUMA: Ali Ndume ya sami kasaitacciyar tarba a Borno ta Kudu

Kuma shi yana ganin kanshi a matsayin jakadan matasa a majalisar, shi ya kara mishi kaimi wajen gabatar da kudurin samar da wannan ma'aikata wacce za 'a samar da itane daga ma'aikatar matasa da wasanni

Sannan kuma cikin yardar Allah idan aka samar da wannan ma'aikata matasan Najeriya za su dara kuma zai zamo sila na yakar talauci da zaman banza a tsakanin matasan.

Honorabul Samaila ya kuma jinjinawa takwarorinshi na majalisa sakamakon goyan baya da suka baiwa kudurin, inda ya ce wannan kuduri ya shafi kowa da kowa ne, domin muddin aka inganta rayuwar matasa toh an inganta rayuwar kowa ne, iyaye maza da mata da sauran jama'ar kasa za suyi maraba da shirin, wanda yanzu abinda ya saura shine Shugaban kasa ya sanya hannu akan wannan kuduri domin zama doka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sadu da wata mai aikin gyaran mota a birnin taraya Abuja

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel