Matasan jihar Zamfara sun koka kan raɗaɗin talauci (Hotuna)

Matasan jihar Zamfara sun koka kan raɗaɗin talauci (Hotuna)

- Wasu gungun matasa sun gudanar da zanga zangar lumana a jihar Zamfara

- Matasan sun koka kan halin kuncin rayuwa da suka ce ake ciki a jihar

Wasu gungun matasa da suka fito daga kungiyoyi daban-daban sun gudanar da wata kwarya-kwaryar zanga-zangar lumana a garin Gusau, babban birini jihar Zamfara.

Jaridar Rariya ta ruwaito matasan sun gudanar da zanga-zangar ne a ranar Talata 18 ga watan Afrilu domin nuna takaicin su akan yadda matsalolin rayuwa suka yi yawa a jihar Zamfara musamman rugujewar bangaren lafiya, kuncin rayuwa ga al'umma da rashin biyan hakkokin ma'aikata.

KU KARANTA: Sojoji sun kashe yan Boko Haram da dama a garin Kala Balge

Bugu da kari matasan sun nuna bacin ransu dangane da rashin aikin yi ga matasa maza da mata na jihar Zamfara, kamar yadda shugaban kungiyar matasan arewa NYA" Kwamred Mannir Haidara Kaura ya bayyana yayin zantawa da manema labaru.

Matasan jihar Zamfara sun koka kan raɗaɗin talauci (Hotuna)

Matasan a yayin zanga zangar

NAIJ.com ta tattaro bayanai da suka nuna cewa an karkare zanga-zangar ne a harabar majalisar dokokin jihar ta Zamfara, inda matasan suka mika koke-kokensu ga shugabannin majalisa. Kuma an kammala zanga-zangar cikin lumana tare da kulawar jami'an tsaro.

ga sauran hotunan:

Matasan jihar Zamfara sun koka kan raɗaɗin talauci (Hotuna)

Matasan yayin zanga zangar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko zaka iya kashe kanka da kan ka?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel