'Yan sanda sun tarwatsa zanga zangar yan shi’a a Kaduna

'Yan sanda sun tarwatsa zanga zangar yan shi’a a Kaduna

- Mabiya addinin shi'a sun gudanar da zanga zanga a jihar Kaduna don a sako musu malaminsu

- Yansanda sun tare su, kuma sun tarwatsa zanga zangar da barkonon tsohuwa

Rundunar 'Yan sandan jihar Kaduna ta tarwatsa yan shi’a a daidai lokacin da suke gudanar da zanga zangaa a jihar Kaduna a ranar Talata 18 ga watan Afrilu, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Yansandan sun yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa gungun magoya bayan shugaban 'Yan Shi'a, Malam Ibrahim El Zakzaky a lokacin da suke gudanar da wani zanga zangar lumana na neman gwamnati ta sako Shugaban nasu.

KU KARANTA: Sojoji sun kashe yan Boko Haram da dama a garin Kala Balge

Rahotanni daga jihar sun shaida ma majiyar NAIJ.com cewa yan shi’an sun fara taruwa ne a kan titin Nnamdi Azikwe da ke yammancin birnin inda a lokacin da suka iso Bakin Ruwa,sai suka hadu da fushin hukuma wanda kuma a karshe aka samu nasarar murkushe masu zanga zangar.

'Yan sanda sun tarwatsa zanga zangar yan shi’a a Kaduna

Masu zanga zangar sakin Zakzaky

Tuni dai kungiyar Shi'ar ta yi Allah wadai da matakin da rundunar 'yan sandan ta dauka a kan mabiyan nata.

Idan ba’a manta ba, tun a shekarar 2015 ne gwamnati ta kama Sheikh El-zakzaky bayan arangama da mabiyansa sukayi da shugaban hafsan sojojin kasa, janar Tukur Buratai, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar yan shi’a da dama tare da kama wasu daga cikinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon ruwan wuta akan yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel