Ya za a kare tsakanin Shugaba Buhari da Sanatoci?

Ya za a kare tsakanin Shugaba Buhari da Sanatoci?

– Ana ta samun rikici tsakanin shugaban kasa da ‘Yan majalisar Dattawa

– An nada Kwamitin sulhu amma har yanzu ba a fara aiki ba

– Shugaban Majalisar yace yana bayan shugaban kasa

Ya za a kare tsakanin Shugaba Buhari da Sanatoci?

Shugaba Buhari a gaban Majalisa kwanakin baya

Kuna da labari cewa an nada kwamiti da zai zauna domin kawo karshen rikicin da ake ta fama tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buahri da kuma ‘Yan majalisar Dattawar kasar tun kwanakin baya.

Kwanaki aka yi ta samun takaddama tsakanin mutanen shugaban kasar da kuma Sanatocin Najeriya musamman game da shugabannin kwastam da kuma EFCC. Har dai ta kai Gwamnatin tarayya ta ke cewa za ta nemi ta shawo kan lamarin don yana ci mata tuwo a kwarya.

KU KARANTA: Babu ranar kare rikicin Buhari da Majalisa

Ya za a kare tsakanin Shugaba Buhari da Sanatoci?

Shugaba Buhari da Sanatoci a wurin liyafa

Shi dai shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa babu wani rikici tsakanin su da shugaban kasa kai-tsaye inda ma ya nemi mutanen Najeriya su kara hakuri su kuma cigaba da marawa Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya yace shi ma yana goyon bayan ta.

Shugaban kasa ya nada kwamiti domin sulhu da Majalisar daga ciki akwai dukkanin Ministocin kasar da su ka taba zama Sanatoci a baya irin su Minista Udoma Udoma, Minista Hadi Sirika, Minista Chris Ngige, Minista Heineken Lokpobiri da kuma Minista Aisha Jummai Alhassan dsr. Sai dai har zuwa Ranar Talata ba su fara wani zama ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

A soke Majalisa gaba daya ko kuwa [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wasu daga cikin al'ummomin garin Abuja ba su dena kashe tagwaye ba - Binciken NAN

Wasu daga cikin al'ummomin garin Abuja ba su dena kashe tagwaye ba - Binciken NAN

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel