Rikicin Sanatoci da shugaban kasa babu ranar karewa

Rikicin Sanatoci da shugaban kasa babu ranar karewa

– Kwanakin baya aka yi ta samun rikici tsakanin shugaban kasa da ‘Yan majalisa

– Har yanzu Kwamitin sulhu da aka nada bai fara aiki ba

– Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ne zai jagoranci kwamitin

Rikicin Sanatoci da shugaban kasa babu ranar karewa

Shugaban kasa Buhari a gaban Majalisa

Kwanaki NAIJ.com ta kawo maku labari cewa an nada kwamiti da zai zauna domin kawo karshen rikicin da ake ta fama tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buahri da da ‘Yan majalisar Dattawa.

Sai dai labari na zuwa mana cewa har yanzu fa babu ranar kawo karshen rikicin don kuwa har yanzu kwamitin da aka nada bai fara aiki ba. Shugaban kasar ya zabi mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin wanda zai jagoranci zaman sulhun.

KU KARANTA: A kara hakuri da Shugaba Buhari Inji Saraki

Rikicin Sanatoci da shugaban kasa babu ranar karewa

Ana rikici tsakanin Sanatoci da shugaban kasa

Wani Sanata yace duk abin ya dame sa don kuwa har yanzu ba a fara maganar zama domin dinke barakar ba. Ko da dai yau aka dawo daga hutu amma har yau ba a fara kawo maganar zaman ba domin a sasanta bangarorin na Gwamnati.

NAIJ.com na samun labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki ya nemi mutanen Najeriya su kara hakuri su kuma cigaba da marawa Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin a tsige Majalisar Dattawa ko kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel