Jin ra’ayin raba gardama: Buhari ya taya al’ummar ƙasar Turkiyya murna

Jin ra’ayin raba gardama: Buhari ya taya al’ummar ƙasar Turkiyya murna

- An kammala zaben jin ra'ayoyin jama'ar kasar Turkiyya a ranar Litinin

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya yan kasar murnan kammala aikin cikin nasara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya gwamnati da mutanen kasar Turkiyya kammala jin ra’a’yoyin mutanen kasar na raba gardama cikin nasara da kwanciyar hankali.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin Kaakakin sa Femi Adesina wanda ya yaba ma shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan sakamakon hangen nesan sa da sanin ya kamata tare da iya tafiyar da al’ummar kasar sa.

KU KARANTA: Matar Sheikh Ibrahim Nyass ta rasu a jihar Kogi (Hotuna)

Buhari yace hakan zai tabbatar da zaman lafiya tare da kawo cigaba mai daurewa a kasar gaba daya, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Jin ra’ayin raba gardama: Buhari ya taya al’ummar ƙasar Turkiyya murna

Buhari tare da Erdogan

A ranar Litinin 17 ga watan Afrilu ne dai aka gudanar da jin ra’a’yoyin yan kasar Turkiyya na raba gardama don tabbatawa ko a akasin haka game da mulkin shugaban kasa Erdogan.

Buhari yace zaben raba gardamar ya nuna manufar yan kasar Turkiyya na cigaba da zama tare da kuma cigaba da nemo hanyoyin ciyar da kasar gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan matan Chibok: Kana tunanin da ake Zahra Buhari aka sace, ya za'ayi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel