Hukumar kula da mahajjata zata horar da mutane 135

Hukumar kula da mahajjata zata horar da mutane 135

- Hukumar kula da mahajjata ta jihar Jigawa za ta horar da mutane 135 domin su horar da maniyyatan masu yin hajjin bana 2017 a jihar

- Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ware kujeru 2,677 ga maniyyatan hajjin bana 2017 a jihar

Hukumar kula da mahajjata ta jihar Jigawa ta shirya wani shirin na rana daya don horar da mutane 135 wadanda kuma za su horar da maniyyatan masu yin hajjin bana 2017 a jihar.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Alhaji Ibrahim Hasheem ya bayyana wannan labari ga manema labarai a Dutse a ranar Talata, 18 ga watan Afrilu.

Hasheem ya ce mutanen 5 da za a horar sun kasance maza 3 da mata 2 wadanda aka zaba daga kowane yankunan kananan hukumomin 27 na jihar domin gudanar da wannan shirin.

Ya kara da cewa mutanen kuma za su gudanar da bita ga maniyyatan a cibiyoyi daban-daban a fadin jihar.

KU KARANTA KUMA: Matar Sheikh Ibrahim Nyass ta rasu a jihar Kogi (Hotuna)

Ya ce kwamitin zai kula da shirin domin tabbatar da cewa kowane maniyyata sun hallarta.

Hasheem ya shawarci maniyyatan da su kasance a cikin horon.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, hukumar Alhazai ta Najeriya ta ware kujeru 2,677 ga maniyyatan hajjin bana 2017 a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon tsohon direban Bishof David Abioye wanda ya karbi musulunci yayin da ya yi murabus da cocin Living Faith Church

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel