Jama’a su cigaba da hakuri da Buhari Inji Saraki

Jama’a su cigaba da hakuri da Buhari Inji Saraki

– Bukola Saraki ya nemi Jama’a su marawa shugaban kasa Buhari baya

– Shugaban Majalisar datttawar ya bayyana cewa wannan Gwamnati na kokari

– Saraki ya kuma nemi a zauna lafiya a kasar

Jama’a su cigaba da hakuri da Buhari Inji Saraki

Mu kara hakuri da shugaba Buhari Inji Saraki

NAIJ.com na samun labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki ya nemi mutanen Najeriya su kara hakuri su kuma cigaba da marawa Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.

Shugaban Sanatocin kasar ya bayyana wannan ne a karshen makon nan lokacin da ya leka gida Ilorin domin hutun bikin Easter. An dai nada Dr. Bukola Saraki a matsayin ‘Baba Addini’ wannan makon.

KU KARANTA: Mun ga canji zuwan Buhari Inji 'Yan Borno

Jama’a su cigaba da hakuri da Buhari Inji Saraki

Ayi ta hakuri da Shugaba Buhari Inji Bukola Saraki

Saraki ya kira al’ummar kasa su kara hakuri da kuma yarda da Gwamnatin shugaba Buhari yace muhimmin abu dai shi ne a zauna cikin zaman lafiya a Najeriya. Saraki yace yana sa rai Jam’iyyar APC za ta cika alkawarun da ta dauka.

Kwanaki shugaban Majalisun kasar ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa yana bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari dari-bisa-dari. Inda ya kuma tattauna game da kuma Ibrahim Magu na Hukumar EFCC.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

APC za ta iya shan kashi Inji wani Dan Jam'iyyar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel