Sojoji sun kashe yan Boko Haram da dama a garin Kala Balge

Sojoji sun kashe yan Boko Haram da dama a garin Kala Balge

- Dakarun sojojin kasa sun hallaka yan Boko Haram su 21 a wani musayar wuta a jihar Borno

- Sojojin Najeriya sun kwato makamai, bamabamai da babura daga hannun yan ta'addan

Rundunar mayakan sojan kasa tace dakarunta dake aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas ta hallaka yayan kungiyar Boko Haram guda 21 a kauyen Jarawa na karamar hukumar Kala Balge, a jihar Borno.

Daraktan watsa labaru na rundunar, Birgediya Sani Usman Kuka Sheka ne ya bayyana haka inda yace “Mayakan runduna ta 3 tare da taimakon mayakan sa kai na Sibilayn JTF sun kai wani samame a ranar 17 ga watan Afrilu a kauyen Jarawa, inda suka yi musayar wuta da yan Boko Haram.

KU KARANTA: Gwamnatin Legas zata hallaka wani Fasto ta hanyar rataya

“A yayin da ake musayar wutan, Sojoji sun kakkabe yan Boko Haram daga kauyukan Deima, Artano, Saduguma, Duve, Bardo, Kala, Bok, Msherde da Ahirde duk a jihar Borno. Sa’annan a yayin karan battan, rundunar ta kashe yan ta’adda 21 tare da ceto mutane 1,623 da Boko Haram ta kama.

Sojoji sun kashe yan Boko Haram da dama a garin Kala Balge

Sojoji suna yi ma kananan yara riga kafi

“Rundunar ta kwato makamai da suka hada da bindiga kirar AK-47 guda 3, nakiya guda 36, adduna 12 da babura 4,” inji SK Usman.

Daga karshe SK Usman yace babu wanda ya mutu daga cikin dakarun sojin da kuma suma yan Sibilyan JTF din.

Sa’annan NAIJ.com ta ruwaito rundunar tana fadin sun mika mutanen da aka ceto zuwa sansanin yan gudun Hijira dake Rann, sa’annan anyi ma kananan yara dake cikinsu alluran riga-kafi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dakarun sojin sama sun yi ma Boko Haram ruwan wuta

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel