“Muddin aka cigaba da tafiya yadda ake yi a Kaduna, APC ba zata lashe jihar ba” – Shehu Sani

“Muddin aka cigaba da tafiya yadda ake yi a Kaduna, APC ba zata lashe jihar ba” – Shehu Sani

-Shehu Sani ya zargi gwamnatin jihar Kaduna da aiwatar da tsare tsaren cutar da jama'a

-Sanatan yayi gargadin muddin gwamnatin ta cigaba da haka, toh APC zata yi asarar jihar

Sanata Shehu Sani yayi gargadin muddin gwamatin jihar Kaduna ta cigaba da aiwatar da tsare tsare masu danne talaka a jihar, toh APC zata yi asarar jihar a zabukan 2019.

Shehu Sani ya bayyana haka ne a ranar Talata 18 ga watan Afrilu yayin dayake ganawa da yan kasuwar barci dake jihar Kaduna, kasuwar da gwamnatin jihar Kaduna ta sha alwashin rusa shi, don sake gina shi a samfurin zamani.

“Ire iren tsare tsaren cin mutuncin mutane da gwamnatin jihar Kaduna ke yi ba zai haifar ma jam’iyyar APC da mai ido ba. A yanzu jama’a sun fara gajiya da APC, Buhari kawai suka aminta da shi.” Inji Shehu Sani

“Muddin aka cigaba da tafiya yadda ake yi a Kaduna, APC ba zata lashe jihar ba” – Shehu Sani

Shehu Sani

NAIJ.com ta jiyo Shehu Sani yana cigaba da fadin: “A yanzu, duk tsare tsaren gwamnatin jihar tana yin su ne don faranta ma wasu mutane kalilan rai.”

Sanatan ya bukaci gwamnatin data dakatar da shirin ta na rushe kasuwar, inda yace rushe shaguna 4800 a wannan marrar da ake ciki zai durkusar da jama’a da dama.

“Ina taya ku alhini, kuma ina rokon gwamnan daya sake duba da wannan manufa tasa. Munyi alkawarin kawo canji ne, don haka ya kamata a dinga tuntubar juna akan muhimman ayyuka.”

“Muddin aka cigaba da tafiya yadda ake yi a Kaduna, APC ba zata lashe jihar ba” – Shehu Sani

Shehu Sani tare da yan kasuwar Barci

Sanata Shehu Sani yace kamata yayi gwamnan ya kammala sauran ayyukan daya dauko:

“Ina mamakin mutumin da bai kammala ko daya daga cikin ayyukan daya dauko ba, amma wai zai rusa kasuwa, idan babu kudin sake gina shi toh ya kenan. Bayan wannan kasuwar na da mutane sama da 30,000 masu cin abinci a cikinta. Ina shawartar gwamnatin data tuntubi yan kasuwar don sanin yaushe ne za’a kammala gina kasuwar.”

Daga karshe Sanatan yace zai aika da takardar koke ga gwamnan akan wannan batu, sa’annan ya shawarci yan kasuwar da su bi ta hanyar majalisar jiha don neman agajinsu kan wannan batu. Bugu da kari Shehu Sani ya shawarci yan kasuwan da cewa zasu iya zuwa kotu, idan gwamnati ta ki jin kukan su.

Shugaban yan kasuwar kasuwar barci Haruna Umar ya shaida ma kamfanin dillancin labaru, NAN, cewa kasuwar nada shaguna 4,800, kuma ana juya sama da naira miliyan 500 a duk rana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda aka yi asara a yayin da gwamnatin jihar Legas ta rusa wata unguwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel