Ana karkatar da akalar maganin cutar sankarau

Ana karkatar da akalar maganin cutar sankarau

- Binciken hukuma a jihar Zamfara, sun nuna yawan wadanda cutar sankarau ta hallaka a jihar kawai, ya karu zuwa mutum 350 daga 215

- Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Muhammad Shinkafi, ya shaida cewa, sun samu korafi daga kananan hukumomin jihar Uku in da ake sayar da maganin cutar ta sankarau ga marassa lafiya, maimakon kyauta

- Gwamnatin jihar ta dauki matakai ciki har da jami'an tsaro, da kuma gudanar da bincike a kan zargin karkatar da akalar magungunan

Binciken hukuma a jihar Zamfara, sun nuna yawan wadanda cutar sankarau ta hallaka a jihar kawai, ya karu zuwa mutum 350 daga 215 a cikin makonni biyun da suka gabata.

Haka ma yawan wadanda suka kamu da cutar ya karu zuwa mutum 3,200 daga 1,800 a cikin wannan lokacin.

Wadannan sabbin binciken sun fito ne a dai-dai lokacin da hukumomin jihar suka kaddamar da bincike kan zargin karkata akalar magungunan cutar a wasu asibitoci.

Ana karkatar da akalar maganin cutar sankarau

Ana karkatar da akalar Maganin cutar sankarau

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi, ya shaida cewa, sun samu korafi daga kananan hukumomin jihar Uku in da ake sayar da maganin cutar ta sankarau ga marassa lafiya, maimakon kyauta.

KU KARANTA KUMA: Har yau na fi ‘Yan matan fim aji – Ummi ZeeZee

Dan haka ne gwamnatin jihar, ta kafa wani kwamiti na musamman domin ya gudanar da bincike a kan gaskiyar lamarin.

Kuma, yanzu gwamnati ta dauki matakai ciki har da jami'an tsaro, da kuma gudanar da bincike a kan zargin karkatar da akalar magungunan.

Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi, ya ce duk wanda aka gano da karkatar da akalar maganin, to ko shakka ba bu za a hukunta shi gwargwadon abinda doka ta tanada.

Daga karshe NAIJ.com ta rahoto cewa, sakataren gwamnatin jihar ya ja hankalin masu irin wannan halayya ta karkatar da maganin cutar ta sanakarau da su ji tsoron Allah su dai na.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Alamomin cutar Kanjamau.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel