Barazanar yunwa na karuwa a Najeriya

Barazanar yunwa na karuwa a Najeriya

- Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi gwamnatin Najeriya cewa, karancin kudade na iya jefa miliyoyin 'yan kasar cikin bala'in 'yunwa nan da makonni masu zuwa

- Hukumar ta bayyana cewa kudaden da ke hannun masu samar da abincin ba za su wuce samar da abincin nan da ranar 18 ga watan mai zuwa ba

Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta ce karancin kudade na iya jefa miliyoyin 'yan Najeriya cikin bala'in 'yunwa nan da makonni masu zuwa. Wannan matsalar dai ta shafi yankin Arewa maso gabashin kasar da ke dauke da miliyoyin 'yan gudun hijira.

NAIJ.COM ta ruwaito cewa, shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce alamu na nunawa miliyoyin 'yan Najeriyar za su fuskanci ja'ibar 'yunwa, lamarin da ya ce ka iya zama babbar matsalar jin kai a duniya.

Wannan dai gargadi ne na yiwuwar samun karancin kudade daga asusun samar da abincin ga kimanin mutane miliyan 4 da dubu 700 da suka fuskanci matsalar tsaro na Boko Haram a kasar.

Wasu daga cikin mutanen da ke zama a sansanonin hijira ma sun tabbatar da karancin abincin. Bayanai na cewa kudaden da ke hannun masu samar da abincin ba za su wuce samar da abincin nan da ranar 18 ga watan gobe na Mayu ba.

KU KARANTA KUMA: Wasika zuwa ga gwamna jihar Borno, Kashim Shettima, abin dake ciki zai kawo hawaye zuwa idanunka

A bayyane yake cewar yankin Arewa maso gabashin Najeriya na kan ganiyar iya fuskantar matsanancin karanci na abinci, sakamakon tsayar da harkokin noma da aka samu bayan da rigimar Boko Haram ta tsanata a yankin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon wasu yara da suka tsira daga hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel