Gwamnatin Legas zata hallaka wani Fasto ta hanyar rataya

Gwamnatin Legas zata hallaka wani Fasto ta hanyar rataya

- Gwamnatin jihar Legas ta fara shirye shiryen rataye wani babban Faston, Fasto King

- Fasto King an kama shi ne da laifin babban mabiyansa yan mata da wuta

Gwamnatin jihar Legas ta shirya tsaf don rataye babban Faston cocin ‘Christian Praying Assembly’ mai shuna Chukwuemeka Ezeugo wanda aka fi sani da lakabi ‘Fasto King’.

Jaridar PM News ta ruwaito a ranar Talata 18 ga watan Afrilu cewar nan bada dadewa ba za’a rataye Faston, kamar yadda kwamishinan shari’ar jihar Legas Adeniji Kazeem ya tabbatar yayin ganawa da manema labaru.

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya yi murabus yanzu – Asu Beks

Majiyar NAIJ.com ta jiyo Kazeem yana cewa: “Nan bada dadewa ba zaku ga matakin da gwamnatin jihar Legas ta dauka kan hukuncin kisan da kotu ta yanke ma Rabaren King da ire irensa.

Gwamnatin Legas zata hallaka wani Fasto ta hanyar rataya

Fasto King

“Akwai mutane da dama dake jiran a zartar musu da hukuncin kisan, ba Fasto King bane kadai. Gwamna Ambode ya umarce ni da inje fursunonin jihar don in tattauna da jami’an dake kula da gidajen yarin.

“Nan bada dadewa ba dai zaku ji matakin da muka dauka, musamman kan wadanda aka yanke ma hukuncin kisa. Amma dai ba zan fada muku takamaimen ranar ba.”

Kimanin shekaru 9 kenan da aka daure Fasto King sakamakon kona wasu yan mata mabiyansa da yayi da wuta saboda sun ki bashi hadin kai a lokacin da ya nemi yayi ta’asa dasu. Daga bisani dukka yan matan sun mutu sanadiyyar ciwon kuna da suka samu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda harsashi ya kashe wata mata a Legas bisa kuskure

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel