‘Ƙidaya 2018: Yakubu Dogara yace ba zata saɓu ba, bindiga a ruwa

‘Ƙidaya 2018: Yakubu Dogara yace ba zata saɓu ba, bindiga a ruwa

- Shirin gudanar da aikin kidayan yan Najeriya ya fara gamuwa da tirjiya

- Yakubu Dogara yace bai kamata ayi shi ba a 2018 ganin cewa zaben 2019 na karatowa

Kaakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya gargadi gwamnatin Najeriya da kada ta kuskura ta gudanar da aikin kidayan al’ummar Najeriya a shekarar 2018.

Dogara ya bayyana haka ne a ranar Litinin 17 ga watan Afrilu inda yace masu fafutukar lallai sai an gudanar da aikin kidaya a shekarar 2018 da su hakura har sai bayan zabe, sakamakon wasu zasu yi amfani da daman don yin magudin kidaya don cimma wata manufa a zabukan 2019.

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya yi murabus yanzu – Asu Beks

Dogara yace gudanar da aikin kidaya a shekarar 2018 ka iya haifar da rudani da rigingimu iri iri musamman ganin yadda zaben shekarar 2019 na karatowa. Don haka ya shawarci a bari har sai bayan zaben 2019.

‘Ƙidaya 2018: Yakubu Dogara yace ba zata saɓu ba, bindiga a ruwa

Yakubu Dogara

Dogara ya bayyana haka ta bakin mai magana da yawunsa, Turaki Hassan, kuma NAIJ.com ta jiyo shi yana fadin: “Ba zan bada shawarar a gudanar da aikin zabe a 2018 ba, na sha fada idan ba za’a iya yin kidaya a 2017 ba, to gaskiya abari har sai bayan 2019, saboda idan aka yi haka, jama’a zasu dage wajen yin magudin alkalumma domin cimma manufar siyasa.

“Don haka nake bada shawara a bari sai bayan 2019, sai gwamnati ta shirya shi, ta haka ne kawai zamu samu kwanciyar hankalin gudanar da aikin yadda ya kamata ba tare da fargaba ba. Na san irin mutanen mu sarai, na san abinda zasu aika. Ina bada shawarar a cigaba da baiwa hukumar kidaya goyon baya su cigaba da shiri har bayan 2019.”

Sai dai hukumar kidaya ta mayar da martani ga maganan Dogara, inda tace wannan ra’ayinsa ne.

Shugaban hukumar Dr isah Yahaya ne ya bayyana haka ga jaridar LEADERSHIP inda yace: “maganan da Dogara yayi, ra’ayinsa ne kawai, amma mu dai muna jiran shugaban kasa ya bamu umarni.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Abinda wani dan Biafra ya fadi zai baka mamaki, kalla:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel